ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, October 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dogon Tattakin Jar Rundunar Sojin Kasar Sin Ruhi Ne Na Jajircewa Da Ake Gadar wa Zuri’o’i

by CGTN Hausa
4 weeks ago

Bana, shekara ce ta cika shekaru 90 da cimma nasarar wani kuduri na kishin kasa da ake wa lakabi da dogon tattaki na jar rundunar sojojin kasar Sin ta gwagwarmayar kwamunisanci. Tattaki ne da aka yi na tsawon kilomita 12,500 cikin shekaru biyu, wanda aka fara da dakarun da yawansu ya kai 206,000, amma guda 57,000 ne kacal suka yi nasarar isa wurin da aka kudurta zuwa.

Wannan tattaki ba labari ne kawai ba, abu ne da yake nuna imani da kuma jajircewa kan cimma wani kyakkyawan buri ba tare da tsoron sadaukarwa kowace iri ba ce, inda sojojin rundunar suka sha gwagwarmayar haye manyan rafuka, da hawan tsaunukan dusar kankara, da kungurman dazuzzuka tare da gwabza yaki da abokan gaba na cikin gida daga bangaren Kuomintang da kuma sojojin mamayar zalunci na kasar Japan. Jar rundunar sojin dake karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi wannan gwagwarmaya ce ba tare da makaman yaki na a-zo-a-gani ba ko kuma rundunar sojin sama mai ba ta kariya ko kuma wata takamaimiyar hanyar kawo musu kayayyakin aiki ba, illa tsantsagwaron ruhin juyin-juya-hali na kishin kasa da ke gudana a jinanen dakarunta.

A kokarinsa na fayyace ma’anar wannan tattaki, wani dan jarida na kasar Amurka, Edgar Snow, wanda ya kasance dan rahoton labarai na yammacin duniya na farko da ya leka sansanin dakarun na kwaminisanci har ya tattauna da wasu dakarun da suka yi wannan tattaki, ya rubuta a wani littafinsa mai suna “Red Star Over China” a shekarar 1937 cewa, ba gwargwamaya ce ta yakin soji ba kawai, amma wata kwarewa ce ta dan’adam da ta kunshi kwarin gwiwa, sanin yadda sabbin wurare suke, gano wani sabon ci gaba, sadaukarwa, nuna biyayya, da tsabagen jajircewa da sauransu.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa, an kammala tattakin tun a shekaru 90 da suka gabata wadda daga bisani aka sauya akalar manufarta daga dabarar soji kawai zuwa wata sabuwar alkibla da ta kai ga samun nasarar juyin-juya-halin Sinawa sakamakon taron Zunyi, amma har yanzu Sinawa suna ci gaba da raya ruhinta na jajircewa. Ana iya ganin misalan haka daga dukkan fannoni na raya ci gaban kasar a yau.

Tun daga kan shugabanni da masu binciken kimiyya da masana da malaman ilimi har zuwa kan masu gudanar da kananan ayyuka, ana dora kishin ci gaban kasa a kan komai. Wannan ya yi matukar taimaka wa kiyaye ci gaban kasar Sin a babban mataki, da hana cin amanar kasa tare da tabbatar da bin doka sau da kafa.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Kazalika, bisa yadda ake ci gaba da tunawa da wannan rana, Sinawa suna gadar da wannan ruhi ga zuri’o’insu na gaba, kamar yadda na ga wani bidiyo na wasu kananan yara daga wata makarantar reno ta kasar, suna kwatanta wani abu na jaruntar jar rundunar sojin kasar Sin ta hanyar wasanni. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

MASU ALAKA

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu
Daga Birnin Sin

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta
Daga Birnin Sin

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Next Post
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

ADC Ta Yi Allah-wadai Da Kama Matasa Masu Gangamin #TinubuMustGo A Borno

LABARAI MASU NASABA

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

October 25, 2026
An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

October 25, 2026
Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

October 25, 2026
Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.