Masu gudanar da masna’antu da kuma masu kananan masana’antu SMEs, da ke gudanar da kasuwancin su a Arewacin Nijeriya, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin jihohi da ke a yankin, da su samar masu da tsare-tsaren da kuma shirye da su sanya su ci gaba da gudanar da kasuwancin su domin kaucewa, durkushewar kasuwancin su a 2025.
Musamman sun bukaci matakan Gwamnatin biyu, da su lalubo msu da mafita, a kan kalubalen tashin samun wutar lantarki a yankin, dakatar da karbar haraji barkatai, lalacewar kayan aiki, rashin tsaro, musaman domin su rage yawan asarar da suke tabkawa, wajen gudanar da kasuwancin su.
- Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutane 20, ‘Yan Kasuwa Da Yara A Benue
- Ko Me Ya Sa Amurka Ta Gaza Cimma Burinta Na Yakin Kimiyya Da Fasaha Da Kasar Sin?
A hirar da ban da ban da jaridar LEADERSHIP da aka wallafa a ranar Lahadi ta yi da ‘yan kasuwar na yankinIn, sun nemi gwamnatocin da ke yankin da su saukaka sabuwar dokar biyan kudin wutar lantarki wacce a cewar su, it ace ke sanyawa ake samu samu ban bancin farashin kudin wutar, a kuma kyale jihohin su gaba da sanya ido kana mar da wutar.
A cewar su, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta mayar da tafiyar da wannan dokar ga hannun Gwamnatocin jihohi, tare da kuma bayar da lasisin bude masana’antu, sanya ido kan karbar hatajin wutar da sauransu.
Tuni dai, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa NERC, ta mika ragamar kula da tafiyar da wutar lantarki ga jihohi shida da suka hada da; Edo, Ekiti, Imo, Ondo, Oyo da Enugu.
Sai dai, abin takaici, babu wata jiha a daya Arewa da ke a cikin irin wannan tsarin na jan raganar kula da tafiyar da wutar lantarkin, a jihohin da ke a yankin.
Kazakila, masu gudanar da masana’antun a yankin, sun yi yakinin cewa, Gwamnatocin da ke yankin, na da karfin da kudaden da za su iya samar da wasu hanyoyin, na samar da wadatacciyyar wutar lantarki, musamman domin a ci gaba da gudanar da masana’antun, duba da yadda baban layin sama da wutar na kasa, ke yawan dakatawa.
A watan Okutoba zuwa watan Nuwambar 2024, sau goma yankunan Arewa Maso Gabas, Arewa Maso Yamma da kuma wasu yankuna na Arewa Maso Tsakiya, takatawar babban layin wutar lantaki ta je fa su cikin duhu biyo bayan hare-haren da ‘yan bindika suka kai a babban layin wutar lantarkin na kasa.
Bugu da kari, masu ruwa da tsaki a fannin sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi, da su wanzar da kasafin kudi na 2025, a kan gaskiay, musamman domin a rage kalubalen da fannin samar da wutar lantarki na kasar ke ci gaba da fuskanta.
Sun kuma yi kira ga matakan gwamnatin biyu, da su rage masu yawan asarar da suke yi, musamman saboda rashin samun wutar lantarki a yankin.
Kazalika, sun bukaci matakan gwamnatin da su taimaka domin a sake farfado da masana’antun da suka durkushe a jihohin Kano, Kaduna da Jos.