Jami’an Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), a safiyar yau, sun kama wata mata dauke da katin zabe 18 a wani samame da suka kai a unguwar Badarwa da ke Jihar Kaduna.
Matar mai suna Maryam Mamman Alhaji, wacce mamba ce a kungiyar goyon bayan daya daga cikin manyan jam’iyyun siyasa, an kama ta da katinan zabe da yawa a hannunta.
- Nishadantar Da Mutane Ya Sa Na Shiga Wasan Barkwanci –Yusuf Abubakar
- Zaben 2023: Tinubu Ya Lashe Akwatin Mazabarsa
An damke ta ne bayan da wasu jami’an tsaro suka yi ikirarin cewa suna da katin zabe kuma suna neman sayar da su.
A yanzu haka dai jami’an hukumar shiyyar Kaduna sun garkame ta, da nufin bankado wasu abokan huldarta wadanda ta ce suna sayen katin zabe ta hanyar biyan kudinsa da PoS.
EFCC ta kuma kama wani mutum bisa zargin sayen kuri’a ta Naira 194,000 a mazabar Gidan Zakka da ke unguwar Goron Dutse a karamar hukumar Dala Kano.
An kuma kama wani jami’in wata jam’iyya da ke siyan kuri’u ta hanyar tura kudi ta banki a yankin Abaji a Abuja.