ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Farashin Mai Aka Rage Ba Tallafi Aka Dawo Da Shi Ba – Gwamnatin Tarayya

by Sadiq
2 weeks ago
Farashin

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa rangwamen farashin man fetur da kamfanin NNPC ya yi ba yana nufin an dawo da tallafin man fetur ba.

Ya jaddada cewa ba a amfani da kuɗin gwamnati wajen rage farashi.

Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arziƙin ƙasa, Taiwo Oyedele ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a.

ADVERTISEMENT

Ya ce NNPC ya rage ribar da yake samu daga sayar da man fetur ne domin yi wa jama’a rangwame, ba wai yana karɓar kuɗi daga gwamnati ba.

A cewarsa, tallafin man fetur yana nufin gwamnati ta yi amfani da kuɗaɗen jama’a wajen biyan wani ɓangare na kuɗin man da ’yan ƙasa za su saya.

LABARAI MASU NASABA

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

Ya ce gwamnatin Tinubu ta kawo ƙarshen wannan tsarin ne a shekarar 2023, kuma ba ta da shirin dawo da shi.

Oyedele ya bayyana cewa NNPC na sayen man fetur daga matatar Dangote da sauran wurare a farashin kasuwa, amma ya rage ribar da yake samu na ɗan wani lokaci domin sayar da man a farashi mai sauƙi ga jama’a.

Ya ƙara da cewa wannan rangwame zai iya amfanar masu sayen mai da gwamnati, domin rage farashi zai kawo ƙarin kwastomomi.

Ministan ya kuma yi watsi da fargabar cewa rangwamen zai ƙara safarar man fetur zuwa maƙwabtan ƙasashe ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce ribar da dillalan man fetur za su samu ba ta kai kashi biyar cikin ɗari na farashin litar mai ba.

Oyedele ya ce sauran matakan da gwamnati ke ɗauka domin rage tsadar sufuri sun haɗa da faɗaɗa amfani da iskar gas ta CNG wajen sufuri, cire haraji da wasu kuɗaɗen shigo da man fetur.

Ya jaddada cewa an tsara waɗannan matakai ne domin rage wa ’yan Nijeriya tsadar rayuwa ba tare da dawo da tallafin man fetur ba.

MASU ALAKA

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin
Manyan Labarai

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

October 25, 2026
Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?
Siyasa

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo
Siyasa

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Yi Watsi Da Nuna Fuska Biyu Da Kuma Amfani Da Yaudarar Siyasa

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Yi Watsi Da Nuna Fuska Biyu Da Kuma Amfani Da Yaudarar Siyasa

LABARAI MASU NASABA

Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta  A Legas

Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta A Legas

October 25, 2026
An Yi Bikin Nune-nunen Hotuna A Nijeriya Bisa Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin

An Yi Bikin Nune-nunen Hotuna A Nijeriya Bisa Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin

October 25, 2026
EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

October 25, 2026
SERAP Ta Kai Gwamnatin Nijeriya Kotu Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 78.8

SERAP Ta Kai Gwamnatin Nijeriya Kotu Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 78.8

October 25, 2026
Malaman Makarantun Gwamnati A Abuja Za Su Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar Litinin

Peter Obi, Marowaci Ne Ba Zai Iya Shugabancin Nijeriya Ba – Wike

October 25, 2026
Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

Wa’adin INEC Ya Ƙare: Ina Makomar Takarar Aminu Gwarzo A Kano Da Pantami A Gombe?

October 25, 2026
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

October 25, 2026
Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

October 25, 2026
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 15 Ta Harin Sama A Borno

October 25, 2026
2027: Hana Tinubu Wa’adi Na Biyu Na Iya Jefa Nijeriya Cikin Rikicin Siyasa — Pakistan

Tinubu Ya Cancanci A Sake Zaɓensa A 2027 — Pakistan

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.