Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi karar gwamnatin jihar kan rashin bayyana sakamakon rahoton hukumar binciken gwamnatinsa daga 2015 zuwa 2023.
Tambuwal wanda ya shigar da karar ta hannun lauyansa, U.O Sulle SAN a gaban babbar kotun jihar Sakkwato ta 6 a karkashin mai shari’a Muhammad Muhammad ya bukaci kotun ta umurci gwamnatin Sakkwato ta fitar da rahoton binciken.
Wadanda Tambuwal ke kara a shari’ar sun hada da Gwamna Ahmad Aliyu da Kwamishinan Shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Sakkwato.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa hukumar binciken gwamnatin Aminu Waziri a tsayin wa’adin mulki biyu a karkashin jagorancin tsohon babban alkalin jihar Gombe, mai shari’a, Mu’azu Pindiga a 2023 domin bin diddgin ayyuka da huldar kudade a gwamnatin Tambuwal.
Hukumar ta gudanar da bincike kan sayar da kadarorin gwamnati, gwanjon motoci, rabon filaye da kuma harkokin kudade da saye da sayarwa na gwamnati daga shekarar 2015 zuwa 2023 tare da kammala bincike a Janairu 2025 tare da mikawa gwamnati rahato a Fabrairu 2026 tare da cewar sun gano almundahanar sama da naira biliyan 117.
Kotun ta bayyana ranar 9 ga Nuwamba 2026 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan buƙatar Tambuwal na tilastawa Gwamnatin Sakkwato bayyana rahoton da hukumar ta yi ikirarin ta gudanar a tsawon wannan lokaci














