Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi gargaɗin cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP har yanzu babbar barazana ne ga tsaro a yankin, duk da nasarorin da sojoji suka samu.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin buɗe taron kwanaki biyu na jami’an tsaro na jihohi da na tarayya a Yola, inda ya buƙaci hukumomin tsaro su ƙara haɗin gwiwa.
Fintiri ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta inganta tsaron iyakoki, samar da kayan aiki na zamani da ƙara kuɗaɗen gudanar da ayyukan hukumomin tsaro.
Ya kuma yi gargaɗin cewa ’yan ta’adda suna amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen ɗaukar matasa aiki da yaɗa bayanan ƙarya.
Gwamnan ya sanar da bayar da gudummawar babura 300 da motocin tsaro 16 domin ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin Jihar Adamawa.
Ya buƙaci jami’an tsaro su samar da hanyoyin magance matsalar ta’addanci a aikace, maimakon dogaro da jawabai kawai.














