Kalmar Fyade kalma ce mummuna mara dadin fada, mara dadin ji mara dadin ba da labari, mara dadin sauraran shari`arsa, sai dai kawai larura da ta tilasta yin haka, domin yakar ta, da kawar da ita a doran kasa, duk da ba ita ce kalma ko laifin da ya fi addabar duniya ba.
Wannan al`amari na fyade, babu wata al`uma a doran kasa da ta yi na`am da shi bisa al’ada ballantana kuma a addini. Aiki ne na masha’a da ke nufin cin zarafi ko tozartawa ko kassara rayuwar al`umma musamman wanda abun ya shafa kai tsaye da ma wanda bai shafa kai tsaye ba, duk masifar fyade na shafar al`umma a wannan duniya ta yau wanda ake da adadin miliyoyin mutane da wannan bala`i ya auka ma ba su ji ba ba su gani ba, Allah ka sauwaka Amin.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 8 A Kudancin Kaduna
- Xi Jinping: Akwai Makoma Mai Haske A Fannin Raya Sana’o’i Na Musamman A Yankunan Karkara
Ma`anar fyade na nufin lalata ko zina ko jima`i ta hanyar nuna karfi da zalinci da rashin tausayi da dabbanci da keta haddin dan adam, mai muni a doran kasa. Ko da ya ke idan ana wannan magana wannan masifa ba ta tsaya a kan Dan’adam ba, a’a har dabba ba su tsallake ba kamar yadda bincike da bayanan masana ya tabbatar da haka. Domun kuwa a hukunci na addini da muke bi (Musulunci) akwai hukuncin wanda ya yi wa dabba fyade domun ko ba a gaya maka ba dabba ba za ta nemi Dan’adam ba, saboda haka ashe tabbatacen abu ne ana ma dabba fyade, Allah ka mana katangar karfe da wannan bala`i wanda har zuwa wannan rubutu ba mu samu bayani da ya tantance adadin masifar da fyade ke janwowa ba.
Da amfadi Kalmar fyade abun da ya fi zuwa wa mai karatu shi ne fyade da kananan yara maza ko mata ko matan aure da zawarawa ko mahaukata ko tsofafun mata, da dai sauran nao`o’i na mutane babu wanda ya kubuta ko yake da tabbacin tsira daga wannan masifa da take bukatar yaka da dukanin karfunmu na tuwo da na hankali, na makamin hukuma, na hikima da ilimi, na dabaru da shara`i da duk wani abu da zamu iya yi domun kawar da wannan masifa a doran kasa.
Wurare da ake iya samun barazana ko afkuwar wannan bala`i ga wanda bai ji ba bai gani ba su ne wurare masu karancin tsaro ko karancin sa idon jama`a. Haka wadanda aka sata ko aka yi garkuwa da su a wannan yanayi na daga cikin masu fuskantar barazanar fade haka irin su kangwaye, ko kufai, kango da gidan da ba a kamala ba, kufai kuma shi ne gari ko gida da wani dalili ya sa aka bar gidan ko garin. Haka wannan wurare irinsu kasuwani tashoshin mota da sauran cibiyoyi masu zaman kansu da na hukumomi na farar hula ne ko na harkar tsaro duk suna da bukatar sa ido sosai ga al`umma a ga wannan bala`i bai afku ba, domun bala`i ne da ke kassara al`umma da mai da ita koma-baya mara kyakyawan fata a rayuwa. Duk wanda wannan masifa ta afka masa sai an tsaya a kansa sosai domun rayuwarsa ta zama mai amfani gare shi da al`umma in ko ba haka ba, tunaninsa zai zama rudadde mai rudarwa, firgitance mai firgitawa, maganin haka daukar matakan da suka dace na tsamo rayuwar wanda ya samu kansa a wannan waki`a ko ibtila`a wato jarabawa ta kaddara ba ta makaranta ba, wanda matasa, ko tsofaffi ko mata da mata, kan aikata ta`asar, Allah ya tsare!
Fyade bai takaita da yin lalata ko jima`i ko zina da karfi ba domun duk abun da aka ce jima`i ko zina ta karfi ana nufin juma`i ba ta hanyar aure ba, wanda ko wacce al`umma ko mabiya addini na da hanyoyin yin aure da yin jima`i tana da yardajiyar hanya ta addininsu ko al`adunsu amma ba fyade ba, kuma ba wai ta wannan hanyar ce kawai ta jima`i ake fyade ba a a akwai hanyoyi da ya kamata jama`a su sa ido sosai wajen lura da dakuna ko shaguna da ke cikin kauyuka ko birane domun gano irin wadanan masu laifi da wasu kan yi amfani da yatsu domun yi wa yara ko ‘yan mata wannan ta`annati na fyade ta hanyar sa yatsa, ko kwakule a al`aurar yara kamar yadda bincike da bayanai suka tabbatar da hakan na faruwa, mai karatu maganar babu da di, wai mahaukaci ya ci kashi. Karin maganar hausawa domun wannan abun ya yi kama da wata Karin Magana ta turawa da ke cewa ‘soft word brooks boons’ wato Magana a baki mai laushi a baki, amma ta ragargaza kasusuwa. Ko kuma inda Malam bahaushe ke cewa tuntuben kashi ba ka fasa kafa ba ka fasa zuciya. Allah ya yi mana gam da katar. Wani ya tabbatar mun cewa an sami wani fajiri da ke bashi sa bacci domin ya yi fyade da shi wanda sai daga baya suka ankarar da shi saboda irin hikimomi da dabaru da siddabaru da mai masa fyaden ke amfani da su!
Kashe-kashen fyade: Abin kan zo ta hanyoyi daban-daban inma a yi fyade da mai rai ko mara rai! haka akwai fyade ta amfani da karfun tuwo ko karfun bindiga ko karfin kujerar mulki ko karfin taron dangi, kai akwai ma fyade da barazanar ba da makin cin jarabawa ko hana makin cin jarabawa idan an ki yarda da fyaden da dai sauran hanyoyi da wannan bala`i kan iya afkuwa bagatatan. Wani shahararen Marubuci, ya tabatar mun da cewa yawan ambaton wannan kalma na kara da bada labarinta na ingiza wannan masifa, ya kenan za a yi? Gaba kura baya siyaki, abu ne dai tabbatace shi ne, hukunci mai karfi mai cike da adalci shi ne maganin wannan matsala.
Matsalar yada cututuka: Daga cikin bala`i da ka iya auka wa jama`a bagatatan shi ne yaduwar cututuka wanda ya yi fyade ga wanin sa mace ne ko namiji ko dabba, ba a san irin cutar da yake da ita ba wanda kuma zai sa ma wanda bai ji ba bai gani ba ko da kuwa dabba ne a kai fyade da shi aka sa mai wata cutar ba a san wanda zai ci namansa ba, da sauran cututukan nan na zamani irinsu kanjamau, cutar sanyi, kyandar biri da sauran cututtuka marasa iyaka da ke haduwa wanda bature ke cewa ‘Communicable diseases’ wanda ko da a aure a wasu jihohin an yi dokoki na gwaji kafin aure, domun kauce wa yaduwar cututuka. Fyade dama aiki ne na ‘yan ta`ada marasa tunani shi ya sa wani mawaki na cewa “ku tashi mu yaki masu fyade suna cutar da `ya`yan mutane domin ko dabbar gida da daji ba sa aiki irin na fyade.”
Abubuwan da ke jawo fyade: Abubuwan suna da yawa kamar shurin masaki, amma a takaice ga kadan daga cikin abubuwan da ke jawo fyade, na farko dai rashin bin dokokin al`ada da na addini na jawo fyade. Misali, shigar tsaraici a makarantu da kasuwanni da kan motsa wa samari ko matasa sha’awa. Haka nan tallace-tallace ga ‘yan mata ko barin yara kanana Maza, da Mata, na gararanba dare da rana. Sai kuma kallon miyagun fina-finai na batsa shi ma na jawo fyade, da barin yara da wasu iyayen ke yi saka-saka su kalli abun da suke so a duk lokacin da su ke so a manyan wayoyi zamani da sauran kafofin sadarwa, shi ya sa dole iyaye su sauke nauyin da Ubangiji ya dora musu ta hanyar ba yara tarbiyya su zama masu nagarta da kishin al’umma da kasarmu ta haihuwa (Nijeriya) mai albarka.
Yadda za a kawar da bala`in fyade: Akwai hanyoyi bila adadin wato masu yawa amman kadan daga ciki su ne, marubuta da ‘yan jaridu su yi aiki tukuru wajen wayar da kan al`umma ta yin amfani da Jaridu kamar yadda muka yi yanzu a wannan Jarida ta hanyar wayar da kan jama`a da zakulo alamu da hanyoyin da wannan bala`i ke afkuwa domun kawar da shi a doran kasa. Dole a yi amafani da Rediyo, Talabijin, Mujallu, Hanyoyin sadarwa na zamani (Social Media), Masallatai, da coci-coci, da sauran wuraran tarurruka na addini da na al’ada da sauran su. A wayar da kan jama`a domun yakar masifar fyade.
A kusan karshe dai babbar hanyar kawar da muguwar dabi’ar fyade da wasu matsafa maketata ko mugaye ko shashashu ke yi ke yi ita ce tabbatar da doka da oda mai cike da adalci, babu cin hanci babu rashawa, ba sani ba sabo kamar yadda na hango a wasu dokoki na Nijeriya (final code), akwai sashi na 358 sai kuma sashi na 283 da aka yi a shekarar 1960, sai kuma sashe na daya biyu cikin baka doka ta 2015 ai da wadanan sassa na dokokin Nijeriya, in har na fahimta za su taimaka wajen dakile fyade.
A karshe idan aka duba yadda wasu kasashe duniya suke da hukuncin kisa ko rataya ga duk wanda kotu ko shari`a ta tabbatar ya aikata laifin fyade, toh, hukunci iri wannan ma hanya ce da za ta iya kawar da matsalar fyade muddun tana cike da adalci yardajje na mahaliccinmu, kamar kasashen irin su Masar, Koriya ta Arewa, Saudiya, Indiya, duk hukuncin kisa ko rataya ake yi idan kotu ta tabbatar mutum ya aikata fyade. Su kuwa irin su kasar Irland, daurin shekara 16 ko dindindin ake yankewa wanda hakan ya yi kama da na kasarmu Nijeriya.
Mustapha Ibrahim Ne ya rubuto daga Kano
Email:[email protected]