ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Ne Ƙarshen Rikicin Yajin Aiki Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya A Nijeriya? (3)

by Sulaiman
9 months ago
ASUU

….ci gaba daga makon da ya gabata

Bayan waɗannan jerin yajin aikin da kungiyar ta aiwatar, ASUU ta kuma tsunduma wani yajin aikin gargaɗi na makonni biyu a ranar 13 ga watan Oktoban 2025 sannan bayan haka, ta bai wa gwamnatin mako guda don biyan buƙatunta.

 

ADVERTISEMENT

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka gudanar a cibiyar ASUU da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da nuna halin ko in kula da buƙatun ƙungiyar.

  • Muhimman Abubuwa 5 Game Da Kasafin Kuɗin 2026 Da Gwamna Raɗɗa Ya Sanya Wa Hannu
  • Amfanin Zogale Ga Lafiyar Jikin Ɗan’adam

Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

 

A yunƙurin biyan buƙatun ƙungiyar, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

 

Tattaunawar Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (ASUU) ta kara zurfafa, inda aka fara sakin Naira biliyan 2.3 ga jami’o’i a fadin kasar a matsayin wani bangare na kokarin magance matsalolin jin dadi da walwalar Malamai a fannin ilimin manyan makarantu.

 

Ministan Ilimi, Dr. Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa, Naira biliyan 2.311 da aka fara fitarwa, yana matsayin albashin rukuni na 8 ne da kuma basussukan kudin karin girma ga ma’aikatan jami’a.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Folasade Boriowo ya fitar ranar Laraba a Abuja.

 

A wani ci gaba daga ɓangaren gwamnatin, an rahoto cewa, Shugaba Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi ta kawo ƙarshen uajin aikin ASUU

 

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya ƙwanƙwashi Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, ɗaliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a nan gaba.

 

Da yake magana da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata, 4 ga watan Nuwamban 2025, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya nemo mafita mai ɗorewa ga duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi a manyan makarantun ƙasar nan.

 

A ci gaba da tattaunawa domin samar da walwala da jin dadin Malaman jami’o’i, gwamnatin tarayya ta yi wa ASUU ta yin karin albashi da kashi 35 amma kungiyar ta yi watsi da wannan tayin inda ta bukaci gwamnatin ta kara hoɓɓasa.

 

Ta kuma bayyana cewa, har yanzu ba a magance muhimman matsalolin da ASUU ta daɗe tana kuka a kansu ba.

 

A wani hoɓɓasa da gwamnatin tarayya ta yi, ASUU ta yi nasarar cimma manyan buƙatunta na yarjejeniyar 2009 Da Gwamnati

 

ASUU ta fitar da wani rahoton nasarori da ta samu kan takaddamar yarjejeniyarta da gwamnatin tarayya ta 2009, inda ta samu sabbin alƙawurra kan ‘yancin kai na jami’o’i, kuɗaɗe, shugabanci, albashi da walwalar ma’aikata.

 

Kungiyar ta ce ɓangarorin biyu sun amince da cikakken ‘yancin kai, aiwatar da dokokin da ake da su kan Majalisar Gudanarwa, tabbatar da nadin mataimakin shugaban jami’a (VC) bisa cancanta da kuma ba da damar gudanar da zaɓuka na cikin gida don shugabancin sashe da malamai.

 

A cikin wata sanarwar manema labarai, da shugaban kungiyar Christopher Piwuna ya sanya wa hannu, ta amince cewa, karatuttukan kafin digiri za su takaita ne ga fannonin kimiyya, kuma yanzu za a riƙa yin ƙarin girma ne bisa ga sakamakon binciken da malami ke yi. Za kuma a cire wa jami’o’i harajin shigo da kayayyakin karatu.

 

Kwamitin aiwatarwa da sashin sa ido na NUC zai kula da aiwatar da wannan yarjejeniyar, tare da yin bita a duk bayan shekaru uku. ASUU ta amince da tsarin albashi da aka gyara wanda ya yi daidai da shawarar Nimi Briggs, yayin da za a biya alawus-alawus da aka samu kowace shekara a kashi 12% na kudin albashin kowace jami’a. An kuma amince da wani sashe na rashin cin zarafin malamai.

 

Wannan sanarwar ta fito ne daga shafin sada zumunta na kungiyar a ranar Talata, 2 ga Disamba, 2025 da tsakar rana.

 

Daga ƙarshe, muna fata gwamnati ta cika sabbin alƙawurran da ta ɗaukarwa kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa don kaucewa barazanar wani sabon yajin aikin.

Asuu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Asuu

An Jinjina Wa Shugaban NPA Kan Rage Cunkoso A Tashar Apapa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.