ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Bas-bas 50 Ga Ƙungiyar Direbobi Ta Zamfara

by Sulaiman
2 months ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa sabbin motocin bas-bas guda 50 ga reshen Ƙungiyar Direbobi ta Ƙasa (NURTW) na jihar, a wani mataki da gwamnatin ta ce na inganta harkokin sufuri da bunƙasa tattalin arziki.

An gudanar da bikin miƙa motocin ne a ranar Laraba a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa gwamnatin jihar ta samar da motocin ne a matsayin rance ƙarƙashin Tsarin Ba da Lamuni na Jihar Zamfara.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin ta ƙara samar da motocin kashe gobara guda biyar domin ƙarfafa ayyukan kashe gobara a faɗin jihar.

Zamfara

Da yake jawabi yayin bikin, Gwamna Dauda Lawal ya ce shirin bayar da motocin a matsayin lamuni wani ɓangare ne na manufofin gwamnatinsa na inganta tsarin sufurin jama’a, ƙarfafa tattalin arziki da kuma tabbatar da ingantaccen kuma amintaccen sufuri ga al’ummar jihar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya ce, an amince motocin za su kasance ƙarƙashin kulawar NURTW, inda ƙungiyar za ta taimaka wajen tantance waɗanda za su amfana, sa ido kan yadda ake amfani da motocin da kuma tabbatar da biyan kuɗin lamunin.

Gwamnan ya bayyana cewa kowace mota ta kai darajar Naira miliyan 27.39, amma gwamnatin jihar za ta ɗauki kashi 20 cikin 100 na kuɗin a matsayin tallafi.

A cewarsa, wannan tallafin ya kai Naira miliyan 5.478 kan kowace mota, yayin da wanda ya amfana zai biya Naira miliyan 21.912 cikin watanni 44 daga ranar karɓar motar.

Gwamna Lawal ya kuma ƙaddamar da motocin kashe gobara guda biyar da gwamnatin ta saya domin inganta aikin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara.

Zamfara

Ya ce, gobara na iya lalata gidaje, shaguna da hanyoyin samun abinci cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, don haka sabbin motocin da aka tanada da kayan aiki na zamani za su taimaka wajen hanzarta kai ɗauki a kowane lungu da saƙo na jihar.

Ya buƙaci jami’an hukumar kashe gobara su ci gaba da horas da ma’aikatansu, wayar da kan jama’a kan hanyoyin kare kai daga gobara, tare da tabbatar da cewa motocin da kayan aikin suna cikin kyakkyawan yanayin aiki a kowane lokaci.

Gwamnan ya jaddada cewa dukkan motocin da aka raba mallakin al’ummar Jihar Zamfara ne, yana mai umartar dukkan ma’aikatu, hukumomi da masu cin gajiyar shirin da su riƙa gabatar da rahoton yadda ake amfani da kadarorin da kuma yadda ake kula da su duk bayan wata uku.

Zamfara

Ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci lalata kadarorin gwamnati, amfani da su ba bisa ƙa’ida ba ko karkatar da su zuwa wata manufa daban ba.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
NSC Ta Ƙaddamar Da Shugabannin Wasannin Masu Buƙata Ta Musamman

NSC Ta Ƙaddamar Da Shugabannin Wasannin Masu Buƙata Ta Musamman

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.