ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar da Matatar Sarrafa Ma’adanin Lithium Ta $200m A Zamfara

by Sulaiman
53 minutes ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ci gaban al’umma ba zai tabbata ba sai idan ana tafiyar da albarkatun ƙasa cikin gaskiya, adalci da inganci, tare da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa masu zuba jari damar gudanar da harkokin su cikin bin doka.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da Matatar Haƙowa da Sarrafa Ma’adinin Lithium ta Zamfara da ke ƙauyen Boko, a Ƙaramar Hukumar Zurmi.An gina matatar ne ta hannun haɗin gwiwar kamfanonin ZAM Mining Company Ltd, Bima Mines Ltd, Jinlide Mining Co. Ltd da wasu abokan hulɗa, kan kuɗin da ya kai dala miliyan 200.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya ce ƙaddamar da matatar wata sabuwar kafa ce ta bunƙasa arzikin Zamfara ta hanyar jawo ingantattun masu zuba jari, haɓaka masana’antu, samar da ayyukan yi da kuma amfani da albarkatun ma’adinai ta hanya mai ɗorewa, tare da sanya jin daɗin al’umma a gaba.

ADVERTISEMENT
Zamfara

Ya ce, tsawon shekaru, Zamfara ta yi fice a matsayin jihar da Allah Ya albarkace ta da ɗimbin albarkatun ma’adinai, amma ya jaddada cewa ainihin albarkar ba ta ta’allaƙa da kasancewar ma’adinan ba, sai dai yadda ake amfani da su wajen inganta rayuwar jama’a.

A cewarsa, tun bayan hawan gwamnatinsa mulki, ta ƙuduri aniyar sauya tsarin harkokin ma’adinai a jihar daga ayyukan da ba su da tsari zuwa ingantaccen tsari na doka, daga anfani ba tare da ƙara ƙima ba zuwa ƙirƙirar darajar tattalin arziki, da kuma daga asarar damammaki zuwa rabon arziki ga jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa

Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

Gwamnan ya ce saboda haka ne gwamnatin jihar ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da za su ƙarfafa haƙar ma’adinai bisa doka, jawo sahihan masu zuba jari, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da cewa harkokin ma’adinai suna bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.Lawal ya ƙara da cewa tattalin arzikin duniya na sauyawa cikin sauri, inda lithium da sauran muhimman ma’adinai suka zama ginshiƙi wajen samar da makamashi mai sabuntawa, motocin lantarki, fasahohin zamani da bunƙasa masana’antu.

Ya ce Zamfara ba za ta ci gaba da kasancewa mai fitar da ɗanyen ma’adinai kaɗai ba, illa sai ta shiga cikin dukkan sassan sarrafa su domin ƙara musu ƙima.

A cewarsa, kafa wannan matata ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta mayar da hankali kan sarrafa ma’adinai a cikin gida, ƙara musu ƙima, horas da matasa ƙwarewa da bunƙasa masana’antu.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa sahihan masu zuba jari cewa gwamnatin Zamfara za ta ci gaba da samar musu da yanayin da zai ba su damar gudanar da harkokinsu cikin nasara.Ya ce gwamnati za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tsaro, inganta ababen more rayuwa da kuma tsara manufofin da za su tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Hakazalika, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani aikin haƙar ma’adinai da ya saɓa wa doka ko wanda zai lalata muhalli ba, yana mai cewa dole ne al’ummomin da ke zaune a yankunan da ake haƙar ma’adinai su amfana kai tsaye.

Lawal ya yi kira ga al’ummar ƙauyen Boko da maƙwabtansu da su ɗauki wannan jari a matsayin haɗin gwiwa domin ci gaba.Ya kuma umarci kamfanonin da ke gudanar da aikin da su bai wa mazauna yankin fifiko wajen samar da ayyukan yi, horas da su sana’o’i, gudanar da ayyukan raya al’umma, kare muhalli da kuma cika nauyin da kamfanoni ke da shi na taimakawa al’umma.

A ƙarshe, Gwamna Lawal ya taya duk masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen tabbatar da wannan aiki murna, kafin ya ayyana a hukumance buɗe Matatar Haƙowa da Sarrafa Ma’adinin Lithium ta Zamfara.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa
  • Sulaiman
    Sin Tana Matsayi Na Farko A Duniya A Fannin Kirkire-kirkiren Wutar Lantarki
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kunnen Doki Da Nijeriya A Gasar Kwallon Kafa Tsakanin Kasashe 4 Ta ‘Yan Kasa Da 17
  • Sulaiman
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Fitar Da Sanarwa Game Da Cika Shekaru 10 Da Fitar Da Hukuncin Takkadamar “Philippines Da China”

MASU ALAKA

Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa
Manyan Labarai

Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa

July 13, 2026
Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato
Manyan Labarai

Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

July 12, 2026
Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027
Manyan Labarai

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

July 12, 2026

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar da Matatar Sarrafa Ma’adanin Lithium Ta $200m A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar da Matatar Sarrafa Ma’adanin Lithium Ta $200m A Zamfara

July 13, 2026
Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa

Sana’ar Ƙosai: Remi Tinubu Ta Yi Kira ga Burna Boy da Davido Su Taimaka wa Talakawa

July 13, 2026
Sin Tana Matsayi Na Farko A Duniya A Fannin Kirkire-kirkiren Wutar Lantarki

Sin Tana Matsayi Na Farko A Duniya A Fannin Kirkire-kirkiren Wutar Lantarki

July 12, 2026
Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

Mahara Sun Kashe Mutane 9 Ƴan Gida Ɗaya, Har Da Jariri Ɗan Wata 2 A Filato

July 12, 2026
Sin Ta Yi Kunnen Doki Da Nijeriya A Gasar Kwallon Kafa Tsakanin Kasashe 4 Ta ‘Yan Kasa Da 17

Sin Ta Yi Kunnen Doki Da Nijeriya A Gasar Kwallon Kafa Tsakanin Kasashe 4 Ta ‘Yan Kasa Da 17

July 12, 2026
FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

FIFA Na Nazarin Faɗaɗa Gasar Kofin Duniya Zuwa Ƙasashe 64

July 12, 2026
Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Sa Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Hajjin 2027

July 12, 2026
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Fitar Da Sanarwa Game Da Cika Shekaru 10 Da Fitar Da Hukuncin Takkadamar “Philippines Da China”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Fitar Da Sanarwa Game Da Cika Shekaru 10 Da Fitar Da Hukuncin Takkadamar “Philippines Da China”

July 12, 2026
Atiku Ya Soki Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC Da NECO Zuwa N50,000

Atiku Ya Soki Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC Da NECO Zuwa N50,000

July 12, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

July 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.