Kasar Sin mai masaukin baki ta yi kunnen doki da ci 1 da 1 da Nijeriya, a zagayen karshe na gasar kwallon kafa ta matasa ta 2026 da aka yi jiya a Yinchuan, wanda ya kawo karshen wasan ‘yan kasa da 17 na sada zumunta tsakanin kasashe 4. kasar Sin ta kammala da nasara a wasa 1 da kunnen doki 1 da kuma shan kaye a wasa 1.
Kasar Sin ce ta bude gasar da ci 3 na nema da Australia, kafin ta sha kashi a hannu Tanzania da ci 2 da nema. Bayan samun maki 4 daga wasanni 3, kasar Sin ta zo ta 2 a gasar, inda Nijeriya ta zo ta 4, bayan ta yi kunnen doki sau 1 da kuma lallasata da aka yi sau 2.
Kocin ‘yan wasan Nijeriya Uwejamomere Eboboritse Omasanjuwa, ya yaba da ingancin gasar, yana cewa, dukkan kungiyoyin su fafata sosai.
1Ya ce “mun fara da karfinmu, kuma mu muka fara cin wasan, sai dai kasar Sin ta sauya dabararta bayan ta sha kaye kuma mun sha wuya wajen tunkarar sauye-sauyen a rabin farko na wasa. Sun kirkiro damarmaki da dama, inda kuma suka farke cin da muka yi musu. Mun yi sauye-sauye bayan hutu, kuma mun yi kokarin tunkararta a rabin karshe na wasan.” (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














