ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

by Abubakar Sulaiman
2 months ago
Daraktan

An yanke wa fitaccen daraktan finafinan Amurka, Carl Rinsch hukuncin ɗaurin watanni 30 a Gidan gyaran hali, bayan an same shi da laifin damfarar kamfanin wallafa fina-finai na Netflix miliyoyin daloli, masu gabatar da ƙara a birnin New York ne suka bayyana hakan a ranar Litinin, Carl ya samu ɗaukaka a fagen fim tun bayan bayar da umurni a fim ɗin ’47 Ronin’ da yayi a shekarar 2013, kamar yadda mujallar FIM ta ruwaito.

Tun a bara ne aka samu Rinsch da laifin karkatar da dala miliyan 11 da kamfanin Netflix suka ba shi a shekarar 2020 domin samar da fim mai dogon zango kan kimiyyar ƙirƙira inji cewar lauyan Gwamnatin tarayya dake Kudancin New York, Jay Clayton, ya ƙara da cewa “Maimakon ya yi amfani da kuɗin wajen shirya fim ɗin, sai Rinsch ya saka su cikin hada-hadar sayen hannayen jari masu matuƙar haɗari da kuma kasuwancin kirifto (cryptocurrency), sannan ya kashe miliyoyin daloli wajen sayen kayayyakin alatu domin amfanin kansa”.

An yi zargin cewa yana samun kuɗaɗen sai ya shiga bushasha abin sa, ya sayi kayayyaki da suka haɗa da tufafın alfarma, kayan ɗaki masu tsada, mota kirar Ferrari, da kuma motoci biyar ƙirar Rolls-Royce, baya ga hukuncin ɗaurin shekara biyu da rabi da aka yanke masa, kotun ta kuma umurci Rinsch, mai shekara 48, da ya mayar da dala miliyan 11 ga Netflix ɗin.

ADVERTISEMENT

Lauyoyinsa sun roƙi kotu da ta sassauta masa hukuncin, suna masu cewa karkatar da kuɗin ya faru ne sakamakon matsin lambar da yake fuskanta a aikinsa da kuma rikicin mutuwar aurensa, koda yake masu gabatar da ƙarar ba su ambaci sunan Netflix kai-tsaye ba, a baya an ruwaito cewa Rinsch ya shiga taƙaddama da kamfanin kan wani fim mai dogon zango da aka fara sanya wa suna ‘White Horse’, amma daga baya aka canja sunan zuwa ‘Conxuest’.

Bisa ga takardun kotu, an tsara labarin fim ɗin mai dogon zango ne kan wani masanin kimiyya da ya ƙirƙiri wasu na’urori (clones) masu ƙarfi, waɗanda aka kora zuwa wani yanki a ƙasar Brazil, a can ne za a ga sun fara haɓaka tare da fara rikici da mutane da kuma tsakanin su, shi dai Rinsch, ya fara shahara ne a matsayin daraktan babban fim ɗin ’47 Ronin’, wanda fitaccen jarumi Keanu Reeɓes ya jagoranta, kafin a yanke masa hukunci, Reeɓes ya rubuta wa alƙalin kotun wasiƙa yana roƙon a yi wa tsohon daraktan nasa sassauci, yana mai bayyana shi a matsayin “ƙwararren mai fasaha” wanda ya jefa kan sa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Daraktan
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Atiku Ya Soki Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC Da NECO Zuwa N50,000

Atiku Ya Soki Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC Da NECO Zuwa N50,000

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.