ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 1, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Bai Wa Sarakuna 19 Sandar Girma Da Motocin Aiki

by Sulaiman
2 hours ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa sandunan girma da motocin aiki ga sarakunan masarautu 19 na jihar, a wani biki da aka gudanar a harabar Cibiyar Baje Kolin Kasuwanci da ke Gusau, babban birnin jihar.

Manyan baƙi da suka halarci bikin sun haɗa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar; Sarkin Nupe da Sarkin Gwandu.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a ranar 31 ga Oktoba, 2026.

ADVERTISEMENT

Bayan rantsar da sarakunan, Gwamna Lawal ya miƙa sandunan girma ga sarakuna 11 masu daraja ta ɗaya da kuma takwas masu daraja ta biyu.

Haka kuma, kowanne daga cikin sarakunan da aka naɗa ya samu motocin aiki guda uku, waɗanda suka haɗa da motar GAC ULTRA SUV samfurin 2025/2026, motar MIKANO ZNA HILUX da kuma motar EV ANTIQUE MODEL (DDP).

LABARAI MASU NASABA

Shinkafi Ya Buƙaci Jam’iyyar APC Ta Yi Adalci A Zaɓen Fidda Gwani

Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano

Gwamnatin jihar ta ce, an samar da motocin ne domin sauƙaƙa zirga-zirgar sarakunan a faɗin masarautunsu, da kuma ba su damar kusantar al’ummomin da suke jagoranta.

Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan biki na nuna yadda gwamnatinsa ke girmama masarautun gargajiya a matsayin muhimman ginshiƙan al’umma, tare da amincewa da rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.

Ya ce bikin ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na bai wa sarakunan gargajiya martaba da goyon bayan hukumomi da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A cewarsa, sandar girma da aka miƙa wa sarakunan alama ce ta ikon da gwamnatin jiha ta damƙa musu, tare da nauyin jagorantar al’ummominsu cikin adalci, hikima, amana da tausayi.

Gwamnan ya buƙaci kowanne sarki da ya gudanar da aikinsa ba tare da nuna bambanci ba, ya tabbatar da adalci, tare da kula da cewa kowa a cikin al’ummarsa yana samun damar kai kukansa da neman shawarwari a fadar masarauta.

Ya ce ya kamata al’umma su riƙa samun shiriya, adalci da kwanciyar hankali daga wajen sarakunansu.

Gwamna Lawal ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na kammala sake gina tare da gyara sauran fadojin sarauta da ba a kammala ayyukansu ba.

Ya ce fadojin na daga cikin muhimman cibiyoyin ikon gargajiya da hulɗa tsakanin shugabanni da al’umma, don haka gyaransu zai ƙarfafa masarautun tare da inganta yanayin gudanar da ayyukan sarakuna.

Dangane da motocin da aka raba, gwamnan ya ce an tanade su ne domin sauƙaƙa wa sarakunan zirga-zirga a masarautunsu, ƙarfafa hulɗarsu da jama’a da kuma inganta haɗin gwiwarsu da hukumomin gwamnati.

Ya kuma gargaɗe su da su kula da motocin yadda ya kamata, tare da amfani da su bisa alhakin da aka ba su na gudanar da ayyukan sarauta.

Gwamnan ya bukaci sarakunan da su gina kyakkyawar alaƙar aiki da haɗin gwiwa tsakanin masarautunsu da gwamnatin jihar, domin cimma muradun ci gaba.

A nasa jawabin tun da farko, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya shawarci sarakunan da aka naɗa da su kasance masu cikakken biyayya ga hukumomin da suke ƙarƙashinsu. Ya kuma bukace su da su mutunta tare da kare martabar masarautun gargajiya yayin gudanar da ayyukansu.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano
  • Sulaiman
    Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido
  • Sulaiman
    2027: Ba Mu Da Matsala Da Takarar Gwarzo, In Ji INEC
  • Sulaiman
    Kwanaki 77: Jam’iyyu Sun Nuna Damuwa Kan Raunin INEC A Shirinta Na Gudanar Da Zaɓe

MASU ALAKA

Shinkafi Ya Buƙaci Jam’iyyar APC Ta Yi Adalci A Zaɓen Fidda Gwani
Labarai

Shinkafi Ya Buƙaci Jam’iyyar APC Ta Yi Adalci A Zaɓen Fidda Gwani

November 1, 2026
kano
Manyan Labarai

Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano

November 1, 2026
Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Ƙara Ƙaimi Wajen Inganta Ayyukan Direbobinsa A Faɗin Afirka
Labarai

Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Ƙara Ƙaimi Wajen Inganta Ayyukan Direbobinsa A Faɗin Afirka

November 1, 2026
Next Post
kano

Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano

LABARAI MASU NASABA

Shinkafi Ya Buƙaci Jam’iyyar APC Ta Yi Adalci A Zaɓen Fidda Gwani

Shinkafi Ya Buƙaci Jam’iyyar APC Ta Yi Adalci A Zaɓen Fidda Gwani

November 1, 2026
kano

Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano

November 1, 2026
Gwamnan Zamfara Ya Bai Wa Sarakuna 19 Sandar Girma Da Motocin Aiki

Gwamnan Zamfara Ya Bai Wa Sarakuna 19 Sandar Girma Da Motocin Aiki

November 1, 2026
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Illolin Rashin Yawan Sha

November 1, 2026
Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Ƙara Ƙaimi Wajen Inganta Ayyukan Direbobinsa A Faɗin Afirka

Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Ƙara Ƙaimi Wajen Inganta Ayyukan Direbobinsa A Faɗin Afirka

November 1, 2026
Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido

Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido

November 1, 2026
2027: Ba Mu Da Matsala Da Takarar Gwarzo, In Ji INEC

2027: Ba Mu Da Matsala Da Takarar Gwarzo, In Ji INEC

November 1, 2026
Yarjejeniyar Zaman Lafiya

2027: Yadda ‘Yan Siyasa Ke Amfani Da Matasa A Bangar Siyasa

November 1, 2026
Kasafin Kuɗin 2027: Tambayoyi Biyar Da Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Amsa

Kasafin Kuɗin 2027: Tambayoyi Biyar Da Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Amsa

November 1, 2026
SAW

Kyawawan Ɗabi’un Annabi Muhammadu (SAW)

November 1, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.