Yayin da ya rage kwanaki 77 kacal a gudanar da babban zaɓen 2027, an fara nuna damuwa kan shirye-shiryen Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), musamman bayan gano wasu hotunan da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI a cikin kundin rajistar masu zaɓe na farko da hukumar ta fitar.
Lamarin ya sake tayar da ƙura da tambayoyi kan sahihancin bayanan masu zaɓe da ke cikin rumbun adana bayanai na hukumar, ingancin hanyoyin da take amfani da su wajen sa ido kan rajista da kuma ƙarfinta na gudanar da zaɓen da zai samu amincewar jama’a.
Haka kuma, damuwar ta ƙaru sakamakon korafe-korafe kan wasu kura-kurai da aka gano a cikin kundin rajistar, ciki har da sunaye, adireshi, jinsi da hotunan da ake zargin AI ne.
Ko da yake INEC ta amince da samun matsalar tare da alƙawarin gyara kundin rajistar kafin fitar da na ƙarshe a ranar 15 ga Disamba, 2026, lamarin ya fallasa wasu giɓi a tsarin yin rajistar masu zaɓe.
Daraktan Sashen Fasahar Sadarwa na Dijital (ICT) na hukumar, Dr Lawrence Bayode, ya bayyana cewa ana zargin wasu jami’an rajistar sun yi amfani da bayanan su na aiki domin shigar da bayanan da ba su dace ba cikin rumbun adana bayanan hukumar.
Sai dai ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa hukumar ta gano waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, kuma tana ɗaukar matakan magance matsalar.














