A Nijeriyar yau, daya daga cikin manyan matsalolin da suka yi tarnaki da zama kafar ungulu ga wanzuwar ingantaccen tsarin mulkin dimokuradiyya shine bangar siyasa a bisa ga yadda ‘yan siyasa ke amfani da matasa wajen sarawa ko babu gaba, tsoratarwa da barazana ga abokan hamayya.
Rayuwar dimbin matasa a Nijeriya ta gurbace tare da shiga mawuyacin hali a dalilin samun kan su a mummunar dabi’ar bangar siyasa da mabambantan ‘yan siyasa ke amfani da su domin biyan kazamar bukatar su wadda babban laifi ne a dokar zabe.
Bangar siyasa matsala ce mai zaman kan ta da ke addabar matasa a Nijeriya tare da kassara rayuwar su a bisa ga yadda suke kasa amfanar kan su ballantana su amfani wasu wanda hakan na nufin bangar siyasa babbar barazana ce ga zaman lafiya da dorewar mulkin dimokuradiyya a kasar nan.
A bayyane yake cewar Nijeriya na cikin kasashen duniya da ke da mafi yawan matasa a inda sama da kashi 60 zuwa 70 suke matasa masu jini a jika ‘yan kasa da shekaru 30 da ke cikin adadin akalla mutane miliyan 230 na al’ummar kasar wadanda galibi rashin aikin yi ke jefa sa su aikata ayyukan assha
Rahotannin baya-bayan nan a 2025–2026, sun nuna cewar duk da raguwar kididdigar rashin aikin yi a hukumance, matsalar rashin aikin yii a tsakanin matasa a Nijeriya, matsala ce mai zaman kan ta wadda rashin magance ta ke kara jefa matasa a ayyukan da ba su dace ba, ciki har da shiga bangar siyasa.
A wani rahoto a 2025 ya bayyana cewa kusan matasa miliyan 80 ne a Nijeriya suke zaman kashe wando ba su da aikin yi wanda ke wakiltar kashi 53% na jimillar matasan kasar, lamarin da ke nuna gagarumar matsalar rashin aikin yi da matasa ke fama a kasar da ta fi kowace kasa yawan jama’a a Afurka.
A yanayin rashin aikin yi, matasa da dama na tsunduma a sabgar bangar siyasa ba wai domin sun zaba ba sai don ba su da wani zabi don haka ya zama tamkar tilas a gare su lamarin da ke zubar da kima da darajar su a cikin al’umma.
Wakilin mu ya ruwaito cewar a yayin da Nijeriya ke shirin fuskantar zaben 2027, an fara ganin alamun tashin hankali a wasu wurare da suka shafi bangar siyasa ta yadda a irin wannan lokaci, galibi matasa ne ke amfani da su wajen aiwatar da ayyukan da ke haifar da tashin- tashina da ke iya jefa su a cikin matsala.
A yayin da matasa ke fama da kuncin rayuwa, wasu ‘yan siyasa da dama na amfani da wannan damar wajen jawo su a cikin sha’anin bangar siyasa ta hanyar amfani da su wajen tayar da tarzoma, haddasa rikita-rikitar siyasa ko tsoratar da abokan hamayya a yayin yekuwar neman zabe ko lokacin zabe. .
Bangar siyasa ta jefa matasa cikin dabi’ar shaye-shaye, kaurwcewa karatu da amfani da miyagun makamai a yayin da ‘yan siyasa suka kebe ‘ya’yansu ga shiga duk wata sabgar bangar siyasa da kwamacalar siyasa.
A bayyane yake yadda ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa ke taka muhimmiyar rawa wajen gurbata tarbiyar matasa a Nijeriya ta hanyar saka su a cikin bangar siyasa, kazamar hanyar da suke amfani da ita wajen kai farmaki ga abokan adawa, a wasu lokutan har da wadanda suke da matsalar rikicin cikin gida.
Hasalima a bayyane yake cewar yadda ake amfani da matasa a bangar siyasa tuni ya zama abin damuwa a kasar, matsalar da a kullum gaba-gaba take kara yi ba tare da ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa sun takawa lamarin burki ba saboda su ke amfana da matasan wajen cin karen su ba babbaka.
A lokutan zabe manya da matsakaitan jam’iyyun siyasa kan yi amfani da matasa a dalilin zaman banzan da suke yi suna ba su kudade kalilan domin su aikata ayyukan tashanci ta hanyar afkawa abokan hamayya a jam’iyyu daban-daban.
A kan wannan masu fashin bakin lamurran yau da kullum na bayyana cewar ya zama wajibi matasa su yi wa kan su karatun- ta natsu su guji shiga harkokin bangar siyasa da duk wani nau’in tashin hankali ko rikici, domin ba abin da take haifarwa face da-na-sani.
A kan wannan gagarumar matsalar, da illar ta ga zaben 2027, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda Olatunji Disu, ya gargadi matasa da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen tayar da tashin tashina a gabanin, yayin ko bayan zabe. Ya kuma ce matasa su guji yada labaran karya, kiyayya ko tsoratar da mutane ta kafafen sada zumunta domin cimma burinsu.
Disu a jawabinsa a wajen wani taro a Abuja a kwana nan ya bukaci matasa da kada su bari a dauke su aikin bangar siyasa domin tayar da hankalin ‘yan siyasa, yin ayyukan daba ko daukar makamai domin biyan bukatun wani dan siyasa.
Maimakon haka, shugaban ‘Yan Sandan ya bukaci matasan da su shiga harkokin zabe a tsarin mulkin dimokuradiyya ta hanyar lumana da bin doka da oda, tare da kare makomarsu wadda ya ce ba tasu kadai ba ce.
Bangar siyasa a kodayaushe kan gurbata rayuwar matasa tare da jefa su a cikin hadarin kamu, rauni ko ma rasa rayuwa domin a dalilin hakan dubban matasa sun halaka. Hasalima sau da yawa, ‘yan siyasar da ke amfani da matasa a irin wannan yanayi ba su damu da makomar su ba, burinsu kawai shi ne cimma muradun siyasar su na dankanen lokaci.
A duk lokacin zabe, kasuwar aikin yi ta daban kan bude ga matasa da ke shiga bangar siyasa domin a bayyane yake cewar ‘yan siyasa da ke fafutukar lashe zabe ko ta halin kaka kan dauki matasa marasa aikin yi ko wadanda ke fama da karancin samun kudiin shiga domin yi musu ayyukan banga.
Galibi abin da ‘yan siyasar ke bukata daga matasan shi ne biyayya da kasancewa a cikin shiri a duk lokacin da aka bukace su aiwatar da wani al’amari na bangar siyasa wanda ake bukatar su aiwatar daidai yadda aka tsara masu.
Ayyukan da ake ba su sun bambanta, domin kuwa wasu a na daukar su domin kuwwar sai wane sai wane, wasu domin tara mutane zuwa tarukan yekuwar neman zabe, wasu kuma su raba kudi ko su rinjayi masu zabe a rumfunan zabe. Sai dai a mafi munin bangaren bangar siyasa shine, akwai ’yan daba da ake amfani da su wajen tsoratar da mutane musamman abokan hamayya, tarwatsa harkokin zabe, tarwatsa akwati, kwacen akwatin zabe har ma da kai hare-haren tashin hankali idan bukatar hakan ta kama.
Kudin da ake ba matasan ba wasu masu yawa ba ne, haka ma a yayin da ake ba wasu nan take, wasu sai sun wahala ake sallamar su. A wani lokaci a na ba su kudi kadan tare da tare da kayan maye.
‘Yan siyasa kan lura da matasan da ke cikin mawuyacin hali, su kuma jawo su a cikin harkar. Da dama daga cikin matasan sun riga sun shiga kungiyoyin matasa a unguwanni wanda hakan ke saukaka tara su cikin gaggawa da kuma samun adadi mai yawa.
Bayan kammala zabe, da zarar an kidaya kuri’u kuma an rantsar da wadanda suka samu nasara, tsarin aiki da matasa a bangar siyasa ya zo karshe. Hasalima matasan kan daina samun wayoyin wadanda suka dauke su aikin, alkawuran da aka yi musu kuwa za su zama tarihi.
Matasan da ke wannan sabgar suna sane da cewar ba a ba su kwangilar aiki, babu tabbacin za a ci gaba da daukar su aiki, sannan babu wata hanya ta shiga sahihiyar harkar siyasa ko samun aikin yi na din-din-din. Alakar da ke tsakanin dan siyasa da dan bangar siyasa ta dogara ne kawai da amfanin da dan siyasar zai samu daga gare shi ta yadda da zarar ya gama amfani da shi, sai ya watsar.
Zaben da a ka gudanar cikin tashin hankali da tilastawa mutane yin abin da ba su so, kai tsaye zabe ne da za a kira maras sahihanci a kundin dokar zabe, haka ma jama’a kan daina sha’awar shiga zabe, yawan masu kada kuri’a kan ragu, sannan amincewar jama’a da tsarin dimokuradiyya zai ja baya.
Amfani da matasa a bangar siyasa ta hanyar sarawa ko babu gaba ya sa tuni jama’a da dama suka dauki zaben a matsayin wani buki kawai na tsarin mulkin dimokuradiyya na cika ka’ida amma ba tare da baiwa jama’a damar zabin abin da suke so ba.
A wajen al’ummomin da abin ya shafa, illar bangar siyasa na bayyana nan take, domin a na hana dimbin mutane kada kuri’a cikin kwanciyar hankali, a na lalata dukiyoy da jikkata mutane da dama kuma a mafi munin yanayi, a na rasa rayuka maras adadi.
Ahmad Baffa, dan siyasa ne da ya ba da shawarar daukar tsauraran matakan hukunta ‘yan siyasar da ke daukar nauyi ko goyon bayan rikicin siyasa gabanin zabe. Ya ce amfani da bangar siyasa babbar illa ce ga dorewar zaman lafiya a siyasar kasar nan.
Baffa ya bayyana cewa karuwar matsalar bangar siyasa a Arewaci da Kudancin kasar nan a kokarin galaba kan abokan hamayya ya kowace irin hanya, matsala ce da ya zama dole a dauke ta a matsayin babbar barazanar ga sha’anin tsaro, ba wai kawai a matsayin tashin hankalin da ke addabar matasa ba.
dan siyasar ya yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na barazana mai tsanani ga dimokiradiyya da kuma zaman lafiyar kasa kamar yadda ya bayyana tare da cewar bangar siyasa babbar barazana ce ga tabbatar da mulkin dimokiradiyya da kuma zaman lafiya a tsakanin al’umma.
“Dole ne a hukunta ‘yan siyasa da ke daukar nauyin bangar siyasa domin abin ya wuce gona da iri. Daga kan kansila, zuwa shugabannin kananan hukumomi, zuwa gwamnoni, da shugaban kasa da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai da na jihohi da duk masu neman zababbun kujeru da jigogin siyasa duka suna da hannu ga tabarbarewar tarbiyar matasa ta hanyar saka su a bangar siyasa.”
A ra’ayin Mahe Alliyu, daya daga cikin matasan da suka samu kan su a bangar siyasa a baya ya bayyana cewar, shiga bangar siyasa shine abu mafi da- na sani da ya yi a rayuwar sa. Ya ce a tsayin shekaru tun daga 2007 da ya fara bangar siyasa, ya bata lokacinsa a banza tare da shiga sabgar shaye- shaye da rashin mutunci, amma da taimakon Allah bayan tuni ya dawo saman hanyar kwarai har ya koma karatu ya kammala jami’a tare da samun aiki a kamfani.
Ya ce babbar matsalar ita ce “dimbin matasa na zaune gida ba aikin fari ballantana na baki, kuma a duk shekara a na yaye dimbin dalibai a jami’oi, kwalejojin ilimi da na kimiyya da fasaha da na aikin jinya da ungozoma wadanda ke komawa zaman kashe wando saboda rashin aikin yi wanda lamari ne da ke jefa rayuwar matasa cikin mawuyacin yanayi ta yadda da yawan su ba su da zabi face shiga bangar siyasa musamman a kakar zabe.”
Masu fashin bakin lamurran yau da kullum sun yi ta nanata cewar idan ba a magance matsalar rashin aikin yi ba, gagarumar matsalar za ta ci- gaba da kara ta’azzarar bangar siyasa da yi wa siyasar Nijeriya illa.
A kan wannan a na ganin samar da ayyukan yi, inganta ilimin fasaha da tallafawa matasa da jari na daga cikin matakan da za su rage dabi’ar bangar siyasa Haka ma masu irin wannan ra’ayin na ganin ya zama wajibi gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su hada kai wajen assasa ayyukan da matasa za su samu aikin yi domin inganta rayuwarsu, matakin da zai taimaka kwarai wajen rage dabi’ar bangar siyasa.














