Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta da wata matsala da takarar ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC, Abdulsalam Gwarzo, inda ta ce umarnin kotu ne ya sa aka cire sunansa daga cikin sabon jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027.
Wani babban jami’in hukumar ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an tantance Gwarzo kuma an amince da takararsa, sai dai ba za a iya wallafa sunansa ba har sai an yanke hukunci na ƙarshe kan umarnin kotu na wucin gadi da Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta bayar a ranar 27 ga Oktoba.
A cewar Jami’in, “Ina tsammanin na gaya muku cewa an tantance shi kuma an amince da shi, sai dai ana jiran hukuncin ƙarshe kan umarnin wucin gadi da Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta bayar a ranar 27 ga Oktoba, wanda ya umarci hukumar kada ta fitar da sunan wani ɗan takarar NDC.
“Ma’ana, ba mu da wata matsala da shi,” in ji jami’in.
Wannan ƙarin bayanin ya biyo bayan binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar a ranar Asabar, wanda ya nuna cewa har yanzu ba a saka sunayen Gwarzo da mataimakinsa, Rabiu Mustapha, cikin sabon jerin sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu da INEC ta fitar ba.














