ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 2, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago

Babban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar APC (APC-PCC) ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nan daram kan alƙawarinsa na kawo ƙarshen biyan kuɗin lantarki bisa ƙiyasin kamfanonin rarraba wutar lantarki, tare da samar da ingantaccen wutar lantarki a Nijeriya.

Mai magana da yawun kwamitin, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026. Ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su yi la’akari da cikakken bayanin da Tinubu ya yi lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, ba wai ɓangaren alƙawarin kaɗai ba.

A wancan lokaci, Tinubu ya ce idan ya gaza cika alƙawarinsa na samar da wutar lantarki da kuma kawo ƙarshen kuɗin ƙiyasin, ya kamata ’yan Nijeriya su ƙi zaɓensa a karo na biyu, sai dai idan ya ba da gamsasshen dalilin rashin cika alƙawarin.

ADVERTISEMENT

Alake ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai daban-daban domin gyara matsalolin ɓangaren wutar lantarki. Daga cikin matakan akwai rattaba hannu kan Dokar Wutar Lantarki ta 2023, wadda ta bai wa gwamnatocin jihohi damar shiga harkokin samarwa, da rarrabawa da isar da wutar lantarki. Ya ce jihohin Legas, Enugu, Abia, Ekiti, Oyo, Kaduna da Neja sun fara amfani da dokar wajen kafa hukumomin kula da wutar lantarki da jawo jarin kamfanoni masu zaman kansu.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta ƙaddamar da Shirin Samar da Mitocin Lantarki na Shugaban Ƙasa domin rage giɓin mitoci da ya ce ya haura miliyan bakwai. A cewarsa, an samar wa kwastomomi sama da miliyan 1.5 da mitoci cikin shekaru uku. Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙoƙarin biyan basussukan da suka taru a ɓangaren wutar lantarki, waɗanda ya ce sun haura Naira tiriliyan shida, tare da ƙaddamar da shirin lamunin gwamnati na Naira tiriliyan huɗu domin biyan basussukan da aka tantance.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano

Alake ya kuma ce an amince da ayyukan gina sabbin tashoshin wutar lantarki guda takwas da inganta wasu huɗu a watan Yunin 2026, baya ga aikin inganta tashoshin TCN guda biyar da aka amince da su a 2024. Ya ce gwamnati na shirin sabunta cibiyar kula da layukan wutar lantarki ta Osogbo da kuma gina babbar hanyar isar da wutar lantarki daga Gabas zuwa Yamma.

Dangane da kuɗin wutar lantarki, ya ce tsarin rarraba kwastomomi zuwa rukunan samun wuta daban-daban an ƙirƙire shi ne domin inganta harkokin kamfanonin rarraba wuta tare da la’akari da ƙarfin biyan kuɗin al’umma.

Sai dai Alake ya amince cewa har yanzu ba a kammala magance matsalolin wutar lantarki a ƙasar ba, yana mai cewa gyaran ɓangaren aiki ne da ke ci gaba. Ya ce Tinubu zai gabatar da bayanan ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar da kuma ƙalubalen da suka rage gaban ’yan Nijeriya yayin neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba
  • Abubakar Sulaiman
    Mahara Sun Kai Hari Shingen binciken Sojoji, Sun Kashe Soja Ɗaya A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

November 1, 2026
kano
Manyan Labarai

Gobara Ta Lalata Shaguna da Gine-gine 110 a Kasuwar Katako ta Kano

November 1, 2026
2027: Ba Mu Da Matsala Da Takarar Gwarzo, In Ji INEC
Manyan Labarai

2027: Ba Mu Da Matsala Da Takarar Gwarzo, In Ji INEC

November 1, 2026

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

Tinubu Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Matsalar Kiyasta Kuɗin Lantarki – APC-PCC

November 1, 2026
Sin Ta Fitar Da Cikakken Tsarin Sauka A Duniyar Wata

Sin Ta Fitar Da Cikakken Tsarin Sauka A Duniyar Wata

November 1, 2026
Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

Sojoji Sun Kashe Ɗan Majalisar Shura Na ISWAP Da Babban Kwamandansa A Borno

November 1, 2026
Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

Ma’aikatar Tsaron Sin Ta Soki Shirin Talabijin Na Japan Mai Suna “VIVANT” Saboda Jirkita Gaskiyar Tarihi

November 1, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Hanyar Neman Bashi Ta USSD Ba Tare Da Intanet Ba

November 1, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Ranar Biranen Duniya

Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Taron Ranar Biranen Duniya

November 1, 2026
Mahara Sun Kai Hari Shingen binciken Sojoji, Sun Kashe Soja Ɗaya A Filato

Mahara Sun Kai Hari Shingen binciken Sojoji, Sun Kashe Soja Ɗaya A Filato

November 1, 2026
An Fitar Da Kudurin Kwamitin Kolin JKS Dangane Da Jagorancin Jamiyyar

An Fitar Da Kudurin Kwamitin Kolin JKS Dangane Da Jagorancin Jamiyyar

November 1, 2026
Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

November 1, 2026
Manzon Musamman Na Shugaba Xi Jinping Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Wasannin Olympics Na Matasa A Dakar

Manzon Musamman Na Shugaba Xi Jinping Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Wasannin Olympics Na Matasa A Dakar

November 1, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.