Gwamnatin Tarayya ta amince da shirin zamanantarwa tare da haɓaka manyan tashoshin jiragen ruwa guda huɗu da ke yankin gabashin ƙasar, a wani ɓangare na ƙoƙarin rage cunkoso da matsin lamba a tashoshin jiragen ruwa na Jihar Legas tare da faɗaɗa ƙarfin kasuwancin teku na Nijeriya.
Ministan Harkokin Jiragen Ruwa da Tattalin Arziƙin Ruwa, Dakta Adegboyega Oyetola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce wannan amincewa ta shafi tashoshin Onne, da Rivers, da Delta da kuma Calabar, bayan wadda aka yi a baya na inganta tashoshin Apapa da Tin Can Island da ke Legas.
Oyetola ya bayyana cewa faɗaɗa shirin zuwa tashoshin da ke wajen Legas zai samar da sabbin hanyoyin gudanar da harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa tare da rage taruwar kaya a yankin Legas. Ya ce: “Wannan amincewa wani muhimmin mataki ne a ƙudurinmu na sauya fasalin kayayyakin more rayuwa a fannin ruwan Nijeriya da kuma buɗe manyan damarmakin tattalin arziƙi da tashoshinmu ke da su.”
A cewar ministan, inganta kayayyakin aiki a tashoshin Onne, Rivers, Delta da Calabar zai taimaka wajen hanzarta sauke kaya, da rage tsawon lokacin da jiragen ruwa ke ɗauka a tasha, da kuma sauƙaƙa jigilar kayayyaki a kan farashi mai sauƙi, kamar yadda yake ƙunshe a cikin manufar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A ƙarshe, Oyetola ya jaddada cewa gwamnati na haɗa aikin zamantar da tsofaffin tashoshin da kuma gina sabbin manyan tashoshin ruwa masu zurfi a jihohi daban-daban, da nufin mayar da Nijeriya babbar cibiyar hada-hadar sufurin teku a nahiyar Afirka.














