Babban daraktan hukumar makamashi na bola jari ta kasa da kasa ko (IRENA), Francesco La Camera, ya bayyana a kwanan nan a hedkwatar hukumar dake birnin Abu Dhabi, fadar mulkin Hadaddiyar Daular Larabawa, cewar kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa ga sauyin makamashi a duniya, da rage fitar da hayakin carbon ta hanyar inganta fasaha, da rage kudin kayan aiki da makamashi mai tsafta da sauransu.
“Gudummawa mafi girma da kasar Sin ta bayar ga sauyin makamashi ita ce, samar wa duniya fasahar makamashi na bola jari mai rahusa, in ji La Camera. Ya kara da cewa, kasar Sin tana inganta fasahar makamashin hasken rana, da makamashi daga karfin iska, da batir da sauransu, lamarin da ya sa kudin kayayyakin da suka shafi wadannan fasahohi ya yi matukar raguwa.
Hakazalika, jami’in ya bayyana cewa, a matakin kasa da kasa, kasar Sin tana samar wa duniya fasaha, da na’urorin makamashin bola jari masu karfin gogayya, wanda ke sa su zama masu araha kuma masu saukin samu. A cikin kasar Sin kuma, tana ci gaba da kara zuba jari a fannin makamashin bola jari, tare da ci gaba da fadada karfin samar da wutar lantarki mai tsafta da ake tarawa. (Bilkisu Xin)














