Ƙungiyar (JIBWIS/Izala) ta mika wani ɗan ƙungiyar agajinta ga Rundunar Ƴansandan Jihar Zamfara sakamakon zarginsa da yin wata waƙa mai ɗauke da kalamai masu tunzura ƙiyayyar addini, inda ake zarginsa da amfani da kalmomin: “Ku ba mu bindigogi mu je mu kashe Kiristoci.”
Kwamishinan Ƴansandan Jihar Zamfara, CP A.M. Bello, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, 2026, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Shalƙwatar Ƴansanda da ke Gusau, babban birnin jihar.
Bayanin Wanda Ake Zargi da Binciken Ƴansanda
CP Bello ya fayyace cewa wanda ake zargin mai suna Umar Ibrahim Gandi Maradun, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Maradun ne a Jihar Zamfara, kuma an haife shi a ranar 15 ga Satumba, 2004. Binciken farko ya nuna cewa ya halarci Makarantar Firamare ta Mualledi Model da Sakandaren Gwamnati ta Rana duk a Maradun.
Ya shiga ƙungiyar agaji ta JIBWIS ne a shekarar 2025, kuma kwanan nan ya samu gurbin karatu don yin Digiri na Farko a fannin Sadarwa (Mass Communication) a Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara.
Rundunar ta tabbatar da cewa an buɗe gagarumin bincike kan lamarin, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin laifukan tayar da hankali, da yunƙurin tada zaune tsaye, da tsoratarwa ƙarƙashin sashi na 77, 78, da 380(b) na Dokar Hunci (Penal Code) da ake amfani da ita a Jihar Zamfara.
Rundunar ƴansandan ta sake jaddada aniyarta ta kare hakkin kowane ɗan ƙasa ba tare da la’akari da addininsa ba, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanada kan ƴancin yin addini da bayyana ra’ayi. CP Bello ya yi fatali da duk wani hali ko kalaman da ke iya haifar da rikicin addini ko barazana ga zaman lafiya.
Rundunar ta yi kira ga shugabannin addinai, da iyaye, da malaman makarantu, da masu ruwa da tsaki da su riƙa tsawatarwa da cusa halayya ta gari ga matasa. Haka kuma ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa jita-jita ko labaran da ba a tabbatar ba da ke iya hura wutar rikicin addini a jihar.














