Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce babu wani tasgaro da aka samu a shugabancin Nijeriya, inda ya ce har yanzu Shugaba Bola Tinubu ne ke jagorantar ƙasar duk da tsawaita hutunsa a ƙasashen waje.
Akpabio ya bayyana hakan ne a Jihar Akwa Ibom a ranar Talata, inda ya ce Tinubu na ci gaba da bayar da umarni da gudanar da ayyukan gwamnati daga ƙasashen waje.
Ya kuma ce ba shi ne Muƙaddashin Shugaban Ƙasa ba.
Ya bayyana tafiyar Tinubu a matsayin hutu na aiki, yana mai cewa Shugaban Ƙasar na ci gaba da gudanar da taruka da sauran ayyukan gwamnati duk da cewar ba ya Nijeriya.
A halin yanzu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, na birnin New York, inda yake wakiltar Nijeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ana sa ran Tinubu zai dawo Nijeriya a ƙarshen makon nan.
Rashin Shugaban Ƙasa da kuma tafiyar Shettima sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Nijeriya da ’yan siyasa kan wa ya kamata a bai wa ragamar shugaban ƙasar na ɗan lokaci.














