Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila, Harry Kane, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ya jagoranci ƙasarsa ta lashe Kofin Duniya, ba wai ya zama wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a gasar ba. Kane ya ce ko da bai lashe kyautar Golden Boot (Takalmin Zinare) ba, muddin Ingila ta zama zakarar duniya, hakan zai fi masa muhimmanci.
Kane, wanda ya zuwa yanzu ya zura ƙwallaye shida a raga a gasar, na biye da Kylian Mbappé na Faransa da Lionel Messi na Argentina, waɗanda kowannensu ke da ƙwallaye takwas. Ingila za ta kara da Norway a wasan kwata-fainal, inda Kane zai fafata da fitaccen ɗan wasan gaba Erling Haaland.
Da yake magana kan karawar da za su yi da Haaland, Kane ya amince cewa ɗan wasan na Norway ƙwararre ne wajen cin ƙwallaye. Sai dai ya ce yana fatan wannan wasa ba zai kasance ranar da Haaland zai yi tasiri kamar yadda ya saba ba. “Erling Haaland na musamman ne wajen zura ƙwallaye, amma ina fatan yau ba zai samu damar yin abin da ya saba yi ba,” in ji Kane.
Kane, wanda ya lashe kyautar Golden Boot a gasar Kofin Duniya ta 2018, ya jaddada cewa burinsa yanzu shi ne ya taimaka wa Ingila ta kawo ƙarshen shekaru kusan 60 ba tare da lashe Kofin Duniya ba. “Babban burina shi ne lashe Kofin Duniya maimakon Golden Boot,” in ji kyaftin ɗin na Ingila.













