ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina

by Abubakar Abba
2 months ago
Cututtuka

Kamar dai yadda Ɗan’adam ke kamuwa da wasu cututtuka a lokacin damina, su ma dabbobi kan iya kamuwa da wasu ire-iren cututtuka daban-daban a lokacin damina.

Wasu daga cikin cututtukan da ke harbin dabbobin a lokacin damina sun haɗa da kamar irin su; waɗanda ke haifar musu da rama, ciwon baki da na ƙafa, inda cutar dabbobin da suka kamu, za su iya yaɗa wa sauran dabbobi.

Matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa kan cututtukan ba, hakan zai iya jawo wa masu kiwon tabka asara.

ADVERTISEMENT

Yana da matuƙar kyau, masu kiwon su riƙa kiyayewa da alamomin cututtukan, musamman domin a ɗauki matakan gaggawa a lokacin na damina.

Kazalika, cutar na kuma harfin ƴan maraƙai da kuma manyansu, kamar irin su sanyi da sauyin yanayi.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

Akwai kuma cutar da ake kira da BƘ, da ƙwayar cutar da ake kira a turance ‘Clostridium’ da ke harbin dabbobin, wanda za ta iya sanyawa dabbobi daga kashi 80 zuwa 100.

Ta fi harbin dabbobi, masu watanni daga tsakanin shida zuwa shekaru biyu.

Alamominta:  Sun haɗa da zazzaɓi mai zafi, rikiɗewar Idanunsu zuwa ja, rage cin abinci da kuma yin tuƙar Ciyawa.

Kazalika, akwai cutar ƙafa da baki, wato a turance ‘Foot and Mouth’, inda ƙwayar cutar da ake kira a turance ta ‘Aphthoɓirus genus’ ke haddasa ta, wacce mafi akasari ta fi harbin shanu.

Alamominta: Sun haɗa da zazzaɓi mai zafi, ramar ƙafa da yawan zubar da miyau, inda daga baya, sai ƙuraje su fito a kan harshensu, kuma ta sanya musu yin ɓarin ciki.

Bugu da ƙari, akwai cutar da ake kira da BRD, wacce ta fi harbin ƙanannan dabbobi, ciki har da ƴan maraƙai.

Akasari, tana afkuwa ne, saboda ƙwayoyin cuta da kuma masu saurin yaɗuwa, inda hakan jawo harbin sauran dabbobi.

Alamominta: Dabbobin da suka kamu da cutar, za su riƙa yawan yin tari, zazzaɓi da kuma yin numfashi da ƙyar.

Alamomin Tsutsar Da Ke Kama Su: Akwai kuma alamomin tsutsa da ke kama su, da suka haɗa da kamar; Kaska da sauransu, inda hakan ke shafar lafiyarsu.

Matakan Kare Su Daga Kamuwa Da Cututtukan:

A cewar wasu likitocin dabbobi, yi wa dabbobin allurar rigafi, a kan lokaci, zai kare su daga kamuwa da irin waɗannan cututtukan.

Misali, dangane da cutar da ke kama baki da ƙafafuwa, musamman shanu, ana buƙatar masu kiwon su riƙa yi musu allurar rigakafi duk bayan wata shida ko kuma sau biyu a shekara.

Ana kuma buƙatar masu kiwon, su tabbatar da sun ɗauki matakan kare yaɗuwar cututtukan daga jikin dabbobin da suka kamu, inda ake so a riƙa wanke ƙafafuwan dabbobin da suka kamu da cutar da ke kama su, a baki da wani sinadarin da ake kira a turance ‘copper sulfate’ da sauransu.

Ana kuma so, dabbobin da kamar kwarkwata ko kaska ta kama, a riƙa shafa musu sinadarin iodine a jikinsu, aƙalla har sau bakwai ko kuma a riƙa shafa musu garin tafarnuwa.

Har ila yau, a riƙa kuma kare dabbobin daga shiga cikin taɓo, a lokacin na damina tare da kuma tabbatar da ana tsaftace wajen kwanansu ta hanyar barin sa a bushe.

Idan har an ankare da duk wata irin alama ta waɗannan ƙwayoyin cututtukan, ana buƙatar masu kiwon su yi gaggawar tuntuɓar likitocin dabbobi.

Waɗanne Matakai Ake Bi Domin Kare Dabbobin Daga Kamuwa Da Cututtuka A Lokacin Na Damnina?

Ana buƙatar masu kiwon su tabbatar da tsaftar dabbobin da ciyar da su abinci mai gina jiki, tabbatar da ana yi musu allurar rigafi, a-kai-a-kai da kuma yi musu wanka da magungunan da ke kashe tsutsar da ke hawa jikinsu.

Kazalika, yana da kyau masu kiwonsu, su riƙa yawan kai su wurin likitocin dabbobi, domin su riƙa duba lafiyarsu, sannan ana kuma so a riƙa ajiye su a wuri mai tsafta.

Bai kuma dace a riƙa ciyar da su da abincin da ya ruɓe ba, ko kuma ruwan shan da ba shi da tsafta.

Ta Yaya Su Kansu Dabbobin Za Su Iya Kare Kansu Daga Cututtuka A Lokacin Damina?

Wasu daga cikin dabbobi da kuma tsintsaye, suna da nasu dabarun da suke kare kansu daga kamuwa da cututtuka a lokacin damina. Misali, wasu na yin amfani da gashin jikinsu, wajen karkaɗe ruwan sama da ya sauka a jikinsu, wanda hakan ke ba su damar busar da jikinsu a kan lokaci.

Wasu kuma, kamar irin su saniya da kuma bujimai, ƙirazansu na da ƙarfi kuma gashinsu na da kauri, inda suke samun shigar iska, ko da kuwa sun jiƙe tare da kuma taimaka musu wajen samun jin ɗumi a jikinsu, inda wasu sauran ƙananan dabbobii a lokacin da ake yin ruwan sama, suke ɓoyewa a ƙarƙashin bishiya, domin samun kariya.

Cututtuka
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
Manyan Labarai

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

September 3, 2026
Cututtuka
Kiwon Lafiya

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

August 30, 2026
Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
Kiwon Lafiya

Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

August 29, 2026
Next Post
Xi Da Kim Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Yarjejeniyar Abota, Hadin Gwiwa Da Taimakon Juna Tsakanin Sin Da DPRK

Xi Da Kim Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Yarjejeniyar Abota, Hadin Gwiwa Da Taimakon Juna Tsakanin Sin Da DPRK

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.