Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, sun ziyarci Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, a Sakkwato.
Kwankwaso ya ce ziyarar ta gudana ne ranar Litinin, jim kaɗan bayan isarsu Sakkwato domin taron ganawa da jama’a gabanin zaɓen 2027.
Ya gode wa Sarkin Musulmi bisa kyakkyawar tarba da kuma shugabancinsa.
ADVERTISEMENT
Ziyarar na daga cikin jerin ganawa da jam’iyyar NDC ke gudanarwa a sassan ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.















