Hukumar ICPC ta sallami wani jami’in tsaro, Daniel Stephen, bayan zargin taimaka wa Aichatou Assabe El-Rufai, matar tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ta shiga harabar hukumar ba tare da bin ƙa’idojin izinin ziyara ba.
Rahoton ya ce an kama jami’in ne bayan bidiyon CCTV sun nuna yadda ya taimaka wa Assabe ta shiga harabar ICPC ta wata ƙofar baya a ranar 5 ga Yuli, 2026. Ana zargin jami’in ya kai ta sashin da ake tsare da El-Rufai, inda ta shafe kusan mintuna 15 tare da shi.
A cikin bayanin da ya rubuta a gaban kwamitin bincike, Stephen ya amince cewa ya taimaka wa matar El-Rufai wajen shiga harabar hukumar ta hanyar da ba ta dace da tsarin tsaro ba. Ya kuma bayyana cewa ya san cewa masu ziyara dole ne a rubuta bayanansu a kofar shiga tare da samun izinin shugaban sashin tsaro.
Rahoton ya ƙara da cewa jami’in ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da ya taimaka wa wasu mutanen da ke da alaƙa da El-Rufai wajen shiga harabar hukumar ta bayan gida ba. El-Rufai yana tsare a hannun ICPC tun ranar 19 ga Fabrairun 2026, bayan an sake shi daga hannun EFCC, yayin da yake fuskantar zarge-zargen karkatar da kuɗaɗe da kuma almundahana da kadarorin gwamnati, zarge-zargen da ya musanta.
Matakin sallamar jami’in na zuwa ne yayin da batun damar iyalan El-Rufai na ganinsa a tsare ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, bayan tsohon gwamnan ya shigar da ƙarar ₦10 biliyan kan ICPC, yana zargin hukumar da hana shi damar ganin matarsa da ɗansa.














