Cece-kuce tsakanin dan takarar Shugabancin Kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan dawo da tallafin man fetur, sake bude bakin iyakokin kasa da kuma batun sahihancin shekarun shugaban kasar, na daga cikin muhawarar batutuwan siyasa da suka fi daukar hankalin jama’a a wannan lokaci.
A cewar Atiku, daukar matakin ya zama wajibi ne domin ragewa ’yan Nijeriya radadin halin kunci da tsadar rayuwa da suke fuskanta sakamakon tsauraran manufofin gwamnatin APC a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu.
Matsayar Atiku ta zo ne bayan da a baya ya sha yin kira da a cire tallafin, lamarin da ya haifar da sabon ce-ce- kucen siyasa kan manufofin tattalin arziki da suka kasance cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar wadanda jama’a ke kuka da su.
Takaddamar tallafin man fetur ta sake daukar sabon salon siyasa ne a yayin da a hukumance Hukumar Zabe ta bude babin yekuwar zaben 2027, yayin da ‘yan adawa ke amfani da bakar kwakwar da ’yan Nijeriya ke sha sakamakon sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu wajen sukar manufofin gwamnatin
Atiku ya ce shirin da yake son aiwatarwa ba wai dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur ba ne kamar yadda ya bayyana a yayin da yake gabatar da shirinsa na farfado da tattalin arziki a 2027.
Ya ce “Ba na son dawo da tsohon tsarin tallafin mai, abin da za yi shine za mu sauya tallafin daga shigo da mai zuwa samar da mai, daga matakin tsaka-tsaki zuwa matatun mai na Nijeriya, sannan daga ikirarin da ba za a iya tabbatarwa ba zuwa samar da gangar mai da za a iya bin diddiginta.” ya bayyana.
A karkashin tsarin da ya ce gwamnatinsa za ta aiwatar idan aka zabe shi, Atiku ya ce matatun mai na gwamnati da masu zaman kansu da suka cika sharudda za su samu danyen mai daga Nijeriya a farashin musamman.
Sai dai ya ce hakan zai kasance ne bisa tsauraran sharudda da suka shafi yawan man da matatar za ta samar, inganci, gaskiya da kuma samar da man da zai shiga kasuwar cikin gida domin amfanin al’umma.
Atiku ya ce za a bayyana adadin kudin da za a kashe da iyakar tallafin, tare da bayyana wadanda za su amfana da shi ta hanyar tantance abin da Nijeriya za ta iya samu kafin ba da tallafi domin tabbatar da abin da zai fita da wanda zai shiga.
Dan takarar na ADC ya ce shirin zai hana wadanda ke da matatun mai amsar danyen mai mai rahusa su ajiye ribar da suka samu ba tare da rage farashin man da suke sayarwa ga ’yan kasa ba. Ya ce za a rika bin diddigin danyen man daga lokacin da aka ware shi, zuwa matatar mai, samar da kayayyakin man fetur, adanawa da kuma kai su kasuwar cikin gida.
Atiku ya ce “idan ka karbi danyen mai na Nijeriya da tallafi, dole ne ka tace shi a Nijeriya, ka samar da kayayyakin da aka amince da su ga ’yan Nijeriya, sannan ka tabbatar sun amfana. In ba haka ba kuwa to ba za ka cancanta da tallafin ba.”
Yayin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku ke bayyana batutuwan a matsayin wasu daga cikin matakan da zai dauka idan aka zabe shi a 2027, gwamnatin Tinubu na kare manufofinta tare da mayar da martani kan ikirarin dan takarar na jam’iyyar adawa
Shugaba Tinubu ya soki matakin Atiku, yana cewar kalamansa sun nuna rashin fahimtar yadda ake tafiyar da gwamnati da kuma tattalin arziiki tare da cewar shawarar Atiku na dawo da tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa alama ce ta rashin sanin kan mulki da tattalin arziki.
Tinubu ya bayyana haka ne a makon jiya a yayin da ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a Fadar Shugaban Kasa yana cewar “Na ga daya daga cikin abokan hamayyata yanzu yana cewar zai dawo da tallafin man fetur wanda hakan ya nuna bai san yadda mulki yake ba.”
Shugaban ya bayyana cewar kafin gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur, jihohi 27 ba su iya biyan albashin ma’aikatansu, ballantana kuma su biya hakkin ’yan fansho.
A cewarsa, gwamnonin jihohi na zuwa Abuja neman taimakon gwamnatin tarayya saboda rashin isassun kudaden tafiyar da jihohinsu lamarin da tuni ya zama tarihi bayan hawansa mulki.
Shugaba Tinubu ya ce yana mutunta damar Atiku ta gabatar da manufofinsa, amma ya bukaci a bayyana yadda za a dauki nauyin tallafin da kuma yadda zai yi aiki a tsarin da ake ciki yanzu. Ya ce dawo da tsohon tsarin tallafin zai iya mayar da kasar cikin matsalar kudade da asarar da aka yi kokarin kawo karshenta.
A yayin da al’ummar kasa ke ci-gaba da tsokaci a kai, gwamnatin tarayya ta ci- gaba da kare cire tallafin, ta na cewar matakin ya taimaka wajen rage matsin lamba kan kudaden gwamnati tare da samar da karin albarkatun da za a iya amfani da su wajen aiwatar da ayyukan ci- gaba.
Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin man fetur ya samarwa Nijeriya da albarkatun da suka kai naira tiriliyan 15.8 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.
A cewar gwamnatin Tinubu daga cikin adadin kudin bakidaya, naira tiriliyan 5.4 ne suka shiga hannun gwamnatin tarayya, yayin da aka rabawa jihohi da kananan hukumomi naira tiriliyan 10.4.
Shugaba Tinubu ya bayyana sanarwar cire tallafin man fetur ne a ranar 29 ga Mayun 2023, a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasa, matakin da ya girgiza al’umma.
Kai tsaye cire tallafin ya sa al’umma suka rika kuka da kokawa musamman tashin farashin man fetur nan take, wanda ya kara tsadar sufuri, abinci da sauran kayayyaki a tsadar rayuwar da jama’a ba su taba fuskanta a baya ba.
Fadar Shugaban Kasa ta ce bisa doka, lokacin da aka tanada domin biyan tallafin man fetur ya kare tun a watan Yunin 2023, saboda haka, kawo karshen tallafin ya zama wajibi domin kare tattalin arzikin kasar da kuma tabbatar da dorewar kudaden gwamnati. Fadar ta ce Shugaba Tinubu ya hanzarta daukar matakin da makonni domin dakatar da ci- gaba da asarar kudaden gwamnati.
A cewar gwamnatin, dawo da tallafin ba abu ne da za a yi kawai ta hanyar sanarwa ba, domin zai bukaci sabuwar doka, tsarin kudade da kuma bayyana inda za a samo kudin da za a rika biyan tallafin.
Gwamnatin ta kuma ce tattalin arzikin man fetur na Nijeriya ya sauya tun daga shekarar 2023, musamman saboda karuwar tace man fetur a cikin gida, ta kuma ce matatar Dangote ta zama muhimmiyar hanyar samar da fetur a cikin gida, kuma tsarin tallafin da ake magana a kai a baya ba zai dace da sabon tsarin kasuwar man fetur ba.
Takaddamar Bude Iyakokin Kasa
Haka ma a yayin da ake cece- kucen tallafin mai, sai kuma Atiku Abubakar ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027, zai sake bude bakin iyakokin Nijeriya da makwabtan kasashe da har yanzu suke a rufe tare da cewar zai samar da manufofin da za su saukaka shigo da kaya da kuma jigilar su a cikin kasar.
Atiku ya ce rufe iyakokin kasar ya tilastawa kamfanoni da ’yan kasuwa da dama rufe sana’o’insu tare da kara tabarbarewar matsalar tsaro a Nijeriya kamar yadda ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo wanda LEADERSHIP Hausa ba ta tabbatar da lokaci da wurin da aka dauki bidiyon ba.
A cewar dan takarar, kasuwancin da ake yi tsakanin kasashe ta kan iyaka halal ne, a kan hakan ya tambayi dalilin da ya sa gwamnati ta rufe iyakokin kasar wanda ya ce matasan da suke da jarin naira miliyan 10 ko 20 kuma suke daukar ma’aikata biyu ko uku sun rasa sana’o’insu saboda rufe iyakokin.
Ya ce “Jihohin Arewa suna da iyaka da Kamaru, Chadi, Nijar da Jamhuriyar Benin, idan aka rufe wadannan iyakoki, matasan da ke yin kasuwanci tsakanin wadannan kasashe za su rasa sana’a, idan mutane sun rasa ayyukansu da abin dogaro da kai, ta yaya za a samu tsaro?” ya tambaya.
Nijeriya ta rufe manyan iyakokinta da makwabtan kasashe a watan Agustan 2019 a zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. A cewar tsohuwar gwamnatin matakin rufe iyakokin, musamman wadanda ke kan iyakar Benin, Nijar, Kamaru da Chadi, na daga cikin matakan da aka dauka domin dakile fasa-kwauri da kare tattalin arzikin kasar.
A nata bangaren, Gwamnatin Tinubu ba ta yi kasa a guiwa ba wajen mayarwa tsohon Mataimakin Shugaba Kasa, Atiku, martani kan alkawarinsa na sake bude iyakokin Nijeriya idan ya lashe zaben shugaban kasa a 2027.
A martanin da ya yi wa Atiku, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce iyakokin Nijeriya ba a rufe suke ba, don haka ba za a ce za a “sake bude” su ba, ya ce gwamnatin Tinubu ta riga ta bude manyan iyakokin kasar, yayin da wasu wuraren ke da takunkumi saboda dalilan tsaro.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta himmatu wajen saukaka zirga-zirga da kasuwanci tsakanin Nijeriya da makwabtan kasashe, amma dole ne a yi hakan cikin tsari da bin dokokin kasar.
Tunji-Ojo ya bayyana cewa ba daidai ba ne a yi wa ’yan Nijeriya bayanin cewa an rufe iyakokin kasar bakidaya. Ya ce akwai wuraren da ake gudanar da bincike da tsauraran matakan tsaro domin hana shigowar makamai domin miyagun mutane za su iya shigowa da abubuwan da za su iya jefa kasar cikin hadari.
Haka kuma, gwamnatin ta ce bude iyakoki ba ya nufin a bar su ba tare da kulawa ba. Ta ce akwai bukatar a daidaita kasuwanci da tsaro domin hana fasa-kwauri, safarar mutane da makamai da sauran laifukan da ake iya aikatawa ta kan iyakoki.
Muhawarar Sahihancin Shekarun Tinubu
Duka baya ga wannan, Atiku Abubakar ya bayyana cewar babu kamshin gaskiya a shekarun da Shugaba Tinubu ke bayyanawa a matsayin sahihan shekarun haihuwarsa, tare da cewar yana da hujjar da zai tabbatarwa duniya shekarunsa 90 kuma zai gabatar da ita a gaban kotu.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa a makon jiya, yayin da yake amsa tambayoyi kan shekarunsa da kuma dalilin da ya sa yake son sake neman shugabancin Nijeriya a zaben 2027. Ya ce shekarunsa bai kamata su zama abin da zai hana shi neman shugabancin kasa ba, domin yana da koshin lafiya da kuzarin gudanar da aiki
Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da ikirarin Atiku a ta bakin Mataimaki na Musamman ga Shugaba Tinubu kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Temitope Ajayi wanda ya ce kofa a bude take ga Atiku da ya je kotu ya gabatar da hujjar da yake ikirarin yana da ita.
Ajayi ya bayyana ikirarin Atiku a matsayin tsananin son zama shugaban kasa, yana cewar mayar da hankali kan shekarun Tinubu da rayuwarsa ta kashin kansa bai dace da wanda ya ce zai gudanar da yakin neman zabe bisa batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Nijeriya ba.
Kakakin Tinubu ya kuma ce kalaman Atiku na zuwa ne a lokacin da ya kasa shawo kan ’yan Nijeriya kan manufofinsa, ciki har da batun dawo da tallafin man fetur a inda ya zargi Atiku da sauya matsayinsa kan wasu manufofi, yana mai cewa ya koma kaiwa Shugaba Tinubu hari da maganganun da suka shafi rayuwarsa ta kashin kan sa wanda ba shine abin da ya kamata ba.














