A wani bincike na likitoci daga Kwalejin Kiwon Lafiya na Cambrige kuma ya bayyana illoli guda goma na kwanciya da barin hagu, sabanin yadda muka kawo wani bincen da ya yi nazari a kan alfanu na kwanciya da barin hagun ba.
Kamar dai yadda aka sani ne, yanayin yadda muke barci; na matukar taka muhimmiyar rawa ga lafiyarmu.
- Matsalar Almajirai Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta Kalubale Ga Shugabannin Arewa – Sultan
- WTO Ta Mai Da Hankali Kan Ci Gaban Da Aka Samu a FOCAC
Don haka, za mu bincika wadannan dalilai guda goma, wadanda bincike ya tabbatar da cewa; suna da illoli ga lafiyar Dan’adam, matukar yana kwanciya da barinsa na hagu.
1- Ciwon Zuciya: Barci da barin hagu, kan sanya zuciya yin aiki a gurguje; wanda hakan kuma, zai iya haifar mata da saurin gajiya, wahala da kuma damuwa.
2- Takurewar Hunhu: Huhu na bangaren hagu, ya fi kankanta; sannan kuma yana kusa da zuciya. Don haka, kwanciya da gefen hagu; zai iya sa wa ya matse ko danne shi.
3- Rashin Jin Dadin Ciki: Kwanciya da wannan bari na hagu, na iya haifar da ciwon ciki ko kuma haifar da ciwon Olsa (Ulcer).
4- Jujjuyawar Hanji: A nan ma, kwanciya da wannan gefe ko bangare na hagu; kan sa hanji ya murmurde ko ya takure a wuri guda.
5- Ciwon Wuya Da Kafada: Kwanciya da barin hagu, na haifar da rashin daidaituwar gabobin jiki; musamman kafadu da sauran sassan jiki, wanda ka iya haifar da ciwon wuya da kuma sauran kafadu.
6- Karkacewar Kashin Baya: Kwanciya da barin gefen hagu, na iya haifar da karkacewar kashin baya.
7- Ciwon Koda: Kwanciya da barin hagu, na kara wa kodar da ke bangaren hagu nauyi tare kuma da kara takure ta.
8- Matsalar Jijiya: Kwanciya da barin hagu, na haifar da matsalar jijiya; ta hanyar taruwar jini a kafa sakamakon takure ta wuri guda.
9- Tattarewar Fuska: Kwanciya da barin hagu, na haifar da tattarewar bari guda na fuska, ta hanyar dora fuskar a kan filo; yau da kullum.
10- Matsalar Wucewar Jini Ta Hanya Guda: Kwanciya da barin hagu, kan haifar da wucewar jini ta hanya daya daga wuya; wanda ka iya haifar da ciwon.