ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Illolin Da Ke Tattare Da Tura Budurwa Zaman Ɗakin Amarya

by Rabi'at Sidi Bala
6 months ago
Budurwa

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da iyayen da suke aurar da ƴa, daga bisani kuma sai su tura ƙanwar yarinyar zuwa gidan amaryar domin ta zauna a can, alhalin tazarar shekarunsu babu yawa, ma’ana dai kusan kansu ɗaya.

Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ko me yake janyo hakan?, ko akwai wasu matsaloli da hakan ke iya haifarwa dalilin zamanta a gidan?,  Wacce shawara za a bawa iyaye?”.

  • Duk Da Rashin Nasara A Hannun Morocco, BUA Ya Bai Wa Super Eagles Kyautar Dala 500,000
  • Muhimmancin Koya Wa ‘Yan Mata Ayyukan Gida Kafin Shiga Gidan Miji

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

ADVERTISEMENT

Sunana Princess Fatima Mazadu, Jihar Goben Nijeriya:

Ana yin hakan saboda kewa da sabo, wani sa’in kuma hakan na haifar da matsala tsakanin ma’aurata ta ɓangaren mazan, shaiɗan zai ta raya musu abubuwa da yawa a kan ƙanwar. Illolin na da yawa kamar; zina da haddasa fitintinu, namiji ya fi sha’awar son zama da ƙanwar fiye da matar tasa, musamman idan ta fi matar sa kyau da kulawa da jikinta ko haiba.

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Takarar Gwamnan Kaduna Na ADC, Ya Gana da El-Rufai, Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Mulkin APC

Yansanda Sun Kai Samame Maɓoyar Masu Laifi, Sun Kama Mutane 150 A Legas

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:

Eh tabbas hakan yana faruwa a wasu lokutan, idan an aurar da yarinya a haɗa ta da ƴar zaman ɗaki, hakan yana sa ita amaryar ta kwantar da hankalin ta kuma yana rage mata kewar gidan su. Tabbas a lokuta da dama ana samun matsalar tsegungumi a wajen irin wannan yara dake jawowa ake samun matsala a tsakanin ma’auratan.

Sunana Marubuciya Nabila Dikko, daga Jihar Kebbi, Argungu Garin kanta:

Budurwa

 

Wasu iyayen suna yi ne domin taimakon kansu da kariya, ko don rage nauyi, suna ganin zaman ƙanwar zai rage musu ɗawainiya, ko za ta tallafa wa amarya. Amma sau da yawa al’ada ce kawai, ba zurfin tunani ba. Yana kawo illah da dama zai iya jawo rikici, hassada, rashin sirrin aure, da kuma lalacewar zumunci, musamman idan shekarunsu kusa ne.

Sunana Jibrin Yusuf Kaila, daga Jihar Jigawa:

Budurwa

A gaskiya wannan abu kuskure ne babba, domin ban ga dalilin da zai sa a taho da ƙanwar amarya wai su zauna tare ba tare da wata hujja babba ba. Mu tuna zuciya bata da ƙashi fa, komai kan iya faruwa tsakanin mijin da ƙanwar amarya, musamman yadda rayuwa ta ɓaci. A tawa fahimtar mafi akasari masu yin haka iyayen amarya ne masu kwaɗayi, domin idan talaka ne angon ba za a taho da ƙanwa ba, tsantsar zarmiya ce da son abin duniya. Irin wannan ne idan dangin miji sun yi ƙorafi sai a yi ta zaginsu. Idan jinya ce sai a kawo dattijuwa ko ma a mayar da ita gidansu. Amma dai ba baligar mace ba. Kai kuma kana gani ba za ka yi magana ba, kai uban amarya.

Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Jihar Neja:

Budurwa

Rashin tunani shi ke janyo hakan, ni ban ga dalilin hakan ba, kusan masu irin ɗabi’ar da-na-sani ce ke biyo baya. Rashin tunanin abin da zai je ya dawo da kuma son zuciya. Ba burgewa bane idan babu dalili mai ƙarfi. Illa na wannan zamani ba iri ɗaya ne da na da ba, tsoron Allah yayi ƙaranci zina ya yi yawa. ko da ita bata neme shi da fasiƙanci ba shi zai iya nemanta ba tare da yayar ta sani ba. Shawarata su bari yin hakan ba burgewa bane kuma ba tsari bane, musamman idan babu wani kwankwarar dalili kamar na rashin lafiya ko haihuwa.

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Budurwa

Al’ada ne domin ɗaukewa amarya kewa da damuwa tare da bata shawarwari akan abubuwan da ka iya faruwa tsakanin miji da mata, a wani lokacin saboda ƙanwa ta riƙa kai bayani akan abin da ke faruwa a gidan amarya da angonta ko kuma tayata aikace-aikacen da ba za a rasa ba na yau da kallum. Matsaloli, tada rigima ko husuma tsakankanin dangi ko miji, saka ganda da kasala wajen aiwatar da aikin gida ga amarya,  Iyaye su kansance masu jan kunnen ƴaƴansu kafin su je gidan, kada su bar su suna jimawa ko su fi kwana 14, mafi tsaka tsakiya shi ne, kwana (21) mafi yawa kwana (30) domin kaucewa da-na-sani da abubuwan da ka iya faruwa mararsa daɗi.

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:

Budurwa

Gaskiya hakan bai dace ba saboda yanayin rayuwa da ake ciki, matsalolin su ne; Za ka iya tarar da mijin yana bibiyar ƙanwar abubuwa dai da dama. Ni dai a shawarata kamar yadda ka tashi ka raine su baka san wacce za ta tafi ba ka ce za ka ɗauki ɗayar ka kai, sai ka yi haƙuri ka riƙe ɗayar a gabanka, Allah ya bata miji ita ma ta yi aurenta. Ni dai ba ni da sha’awar hakan, domin na ga illolinsu daban-daban da yawa.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rabo A Jihar Kano:

Budurwa

Wasu iyayen suna yin hakan ne wai domin ƙarfafa zumuncin yaran, wasu kuma kwaɗayi ne. Kwarai kuwa akwai matsaloli domin dukkansu yara ne, tarbiyar ƙaramar za ta zama wata iri. Sannan hakan zai iya haifar da wata matsalar a zaman ita yayar da mijinta. Gaskiya ya kamata su daina tura ƙannan yaran da aka yi aurensu gidajen mazan ba, musamman yaran da suka kai munzalin balaga, domin a garin ƙarfafa zumuncinsu zai iya wargaza zumuncin nasu.

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos a Jihar Filato:

Budurwa

Darasin wannan mako yana da muhimmanci, musamman ga iyaye. Lallai ne iyaye su sani cewa wannan tsohuwar al’ada ta kai ƙanwa ko ƴar’uwa don zaman ɗaki ta haifar da matsaloli da dama a baya, wanda ya kamata yanzu a ce an daina ta. Kodayake al’ada ce da aka faro ta da nufin ɗebe kewa ga amarya da aka kaita wani baƙon gida ko gari. Sannan kuma ta samu ƴar aika don wasu hidimomin gida. Amma daga bisani matsaloli na cin amana, cin zarafi da sauransu sun sa al’adar ta fara mutuwa, sai har yanzu wasu suna cigaba da yi. Don haka ina mai ba da shawarar a dakatar da irin wannan al’ada, don kaucewa lalata abin da ake samar na alheri.

Sunana Anas Bn Malik, Achilafia

Budurwa

Wasu iyayen suna ganin ƙanwar za ta koyi tarbiyya da rayuwar aure daga yayarta, haka kuma ana yin hakan ne don rage wa amarya wahalar ayyukan gida. Amma idan shekarunsu kusan ɗaya ne, hakan na iya zama ba daidai ba a hankali da tunani. Matsaloli; rashin ƴanci da matsin lamba a gare ta, rikici, hassada, ko fahimtar juna ba daidai ba, tasiri mara kyau ga tarbiyya da tunanin matashiya, zargi ko magana daga jama’a, ko da babu laifi. Shawara ga iyaye; su yi la’akari da shekarunta da balagaggen tunaninta. Kar a tura yarinya sai da larura ta gaske da tsauraran ka’idoji.

Sunana Abubakar Usman, Malam Madori, A Jihar Jigawa:

Budurwa

Wasu iyayen suna yi bisa niyyar taimakawa amarya wajen sabuwar rayuwar aure, rage mata kewa, ko samun taimako a ayyukan gida. A wasu lokuta kuma, al’ada ce ko rashin yarda da mijin ne ke sa hakan. Matsaloli; kishi, rikici, zargi, da kuma hana kanwar samun damar ci gaba da rayuwarta da walwala. Shawara iyaye su kauce haɗa ƴaƴansu a gidan aure guda, musamman idan shekarunsu na kusa da na ƴar’uwarta. Iyaye su mayar da hankali kan tarbiyya mai kyau, basu shawarwari da goyon baya daga nesa, fiye da tilasta su zama tare da mijin ƴar’uwarsu.

Sunana Idris Haruna Zareku, Miga, A Jihar Jigawa:

Wasu iyaye suna haɗa ƙanwarta da amarya ne domin ta taimaka mata a gidan, ta koyo rayuwar aure, kuma ta zama abokiyar zama domin amarya kada ta ji kaɗaici, musamman idan sabuwar aure ce. Haka kuma yana jawo saɓani tsakanin miji da mata. A shawar ce mafi alheri, a bar amarya da mijinta su fara zaman aure su kaɗai.

Budurwa
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Labarai

Ɗan Takarar Gwamnan Kaduna Na ADC, Ya Gana da El-Rufai, Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Mulkin APC

July 7, 2026
'yansanda
Labarai

Yansanda Sun Kai Samame Maɓoyar Masu Laifi, Sun Kama Mutane 150 A Legas

July 7, 2026
Sabbin Ministoci
Labarai

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Nuna Damuwa Kan Yawaitar Hare-haren Da Ake Kai Wa Jami’an Soji

July 7, 2026
Next Post

Buƙatar Sanya Ƴanmata A Kan Sana'a Kafin Aurar Da Su 

LABARAI MASU NASABA

Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

Rahoton Bankin Duniya: Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Dore

July 7, 2026
Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi

Binciken CGTN Ya Shaida Kiraye-kirayen Jama’a Game Da Bukatar Hada Karfi Da Karfe Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsanantar Yanayi

July 7, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai

Ɗan Takarar Gwamnan Kaduna Na ADC, Ya Gana da El-Rufai, Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Mulkin APC

July 7, 2026
Kulla Yarjejeniyar UNCLOS Da Aiwatar Da Ita Jigo Ne Na Wanzar Da Gaskiya Da Adalci A Odar Teku Tsakanin Kasa Da Kasa

Kulla Yarjejeniyar UNCLOS Da Aiwatar Da Ita Jigo Ne Na Wanzar Da Gaskiya Da Adalci A Odar Teku Tsakanin Kasa Da Kasa

July 7, 2026
Argentina Ta Kai Zagayen Kwata Fainal Bayan Nunawa Egypt Ƙwanji

Argentina Ta Kai Zagayen Kwata Fainal Bayan Nunawa Egypt Ƙwanji

July 7, 2026
Gwajin Harba Makamai Masu Linzami Aiki Ne Na Horarwa Da Sojojin Kasar Sin Ke Gudanarwa

Gwajin Harba Makamai Masu Linzami Aiki Ne Na Horarwa Da Sojojin Kasar Sin Ke Gudanarwa

July 7, 2026
'yansanda

Yansanda Sun Kai Samame Maɓoyar Masu Laifi, Sun Kama Mutane 150 A Legas

July 7, 2026
Wakiliyar Sin Ta Bayyana Matsayar Kasar Yayin Taron Muhawarar Gaggawa Dangane Da Sudan

Wakiliyar Sin Ta Bayyana Matsayar Kasar Yayin Taron Muhawarar Gaggawa Dangane Da Sudan

July 7, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Nuna Damuwa Kan Yawaitar Hare-haren Da Ake Kai Wa Jami’an Soji

July 7, 2026
Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Kan Ayyukan Rigakafin Ambaliyar Ruwa Da Karfafa Ceton Jama’a

Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Kan Ayyukan Rigakafin Ambaliyar Ruwa Da Karfafa Ceton Jama’a

July 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.