ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iran Ta Musanta Zargin Ɓoye Makaman Nukiliya A Dutsen Kolang

by Sulaiman
2 months ago
Iran

Iran ta sake musanta zargin cewa tana da wani ɓoyayyen wurin gudanar da ayyukan nukiliya a Dutsen Kolang, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kai hari kan wurin da ke tsakiyar ƙasar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba cewa, “Yawan mayar da hankali da Washington ke yi kan Kolang Kouh, inda babu wani aikin nukiliya da ake gudanarwa, ba komai ba ne face wata hujja ta ƙarya da aka ƙirƙira domin kai hari, lalata abubuwa da kuma cigaba da tada zaune tsaye.”

Ya kuma jaddada cewa Iran ta bayyana dukkan ayyukanta na nukiliya ga Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IAEA).

ADVERTISEMENT

A ranar Talata, Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta kai hari kan wurin, wanda ake kira Pickaxe Mountain da Turanci.

A shekarar 2025, wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka, ciki har da The Washington Post da The New York Times, sun ruwaito cewa Iran ta hanzarta aikin gina wani ɓoyayyiyar cibiyar nukiliya ta ƙarƙashin ƙasa a Dutsen Kolang. Sai dai Tehran ta musanta rahotannin.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Dutsen Kolang na kusa da cibiyar nukiliyar Natanz ta Iran, wadda Amurka ta kai wa hari a lokacin wani taƙaitaccen yaƙi da aka yi a watan Yunin shekarar 2025.

Iran
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

MASU ALAKA

Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
Labarai

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Labarai

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Next Post
Asibitin Tafi Da Gidanka Na Jirgin Ruwan Sin Ya Nufi Kasashen Afrika Da Kudancin Asiya Domin Bayar Da Hidimomin Jin Kai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Iran

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Iran

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.