Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan harkokin tsaro (ONSA) ta ce, bisa azama da himmar hadakar jami’an tsaron soji, ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro hakan ya kai ga nasarar kawo karshen ‘yan ta’adda 8,034 a shekarar 2024.
Har ila yau, ONSA ta ce, ayyukan hukumomin ya kuma kai ga cafke mutum 11,623 da ake zargin ‘yan ta’adda ne kari da ceto mutane 7,967 da aka yi garkuwa da su a shekarar 2024.
- Mun Karbi Rancen Dala Biliyan 1 Don Tallafa Wa Matatar Man Dangote —NNPC
- Dakarun MNJTF Sun Daƙile Harin Da Aka Kai Sansanin Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10 A Kamaru
Daraktan kwamitin lamuran shari’a da dabarun sadarwa na ofishin Mashawarcin Shugaban Kasan, Zakari Mijinyawa, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin a Abuja.
Mijinyawa ya kara kuma da cewa yunkurin jami’an tsaron ya kuma haifar da sakamakon mai kyau na kwato makamai 10,200 da alburusai 224,709 daga hannun ‘yan ta’addan dukka a 2024.
A cewarsa, adadin mutum 30,313 wadanda ake zargi da manyan laifuka ne aka kama, yayin da kuma aka kwato motocin sata guda 1,438 a hannun ‘yan ta’addan cikin 2024.
Ya kuma kara da cewa yunkurin jami’an tsaron a 2024 ya kai ga dakile satar mai da darajarsa ya kai naira biliyan 57 da kuma taimakawa wajen tabbatar da samun nasarar kara hako mai zuwa ganga miliyan 1.8 a kowace rana.
Mijinyawa ya ce, bisa burin fadar shugaban kasa an samu nasarar rage satar danyen mai a yankin Neja Delta.
Ya kuma ce hukumar kula da gyaran tarbiyya (NCoS) ta tsare da kare mutunci da kimar fursunonin 80,000 tare da kula da masu laifukan 50,000. Ya kara da cewa an horas da fursunoni sama da 30,000 sana’o’in hannu, fursunoni 2,000 sun zana jarabawar kammala sakandari, yayin da wasu 1,000 suka kammala karatun diploma da digiri a jami’ar karatu daga gida (NOUN).