ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Nijeriya Ta Himmatu Wajen Inganta Tsarin Karatun Allo

by Bello Hamza
9 months ago
Allo

Gwamnatin Tarayya, ta sha alwashin tabbatar da inganta tsarin koyar da karatun Allo da yadda ake gudanar da ilimin tsangayu a faɗin ƙasar.

Ministan Ilimi na Nijeriya, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan biyo bayan taron ƙaddamar da tsarin inganta koyar da Karatun Allo da ilimin Tsangayu na bai-ɗaya, wanda ya gudana a ranar Litinin din da ta gabata, a Babban Birnin Tarayya Abuja.

  • EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja
  • Rikicin PDP Ne Ya Sanya Ni Komawa Jam’iyyar Accord – Adeleke

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske dangane da wannan gagarumin sauyi da ma’aikatar ilimin ke ƙoƙarin aiwatarwa, mai taimaka wa Ministan ilimin kan ilimin Almajirai da Tsangayu da da Makarantun Allo, Dakta Balarabe Shehu Kakale, ya ce nan ba da jimawa ba Makarantun Allo za su dinga gogayya da takwarorinsu na Boko da ke faɗin ƙasar.

ADVERTISEMENT

Kakale, wanda shi ne Barden Tsangayu da Makarantun Allo na Ƙasar Hausa, ya ƙara da cewa manufar samar da tsarin shi ne don ingata rayuwar Almajiran da ke lungu da saƙo na Nijeriya.

A cewar Dakta Kakale, “Kafin a kai ga wannan matsaya, sai da muka karaɗe ɗaukacin shiyyoyin siyasa shida na Nijeriya, inda muka tattauna da masu ruwa da tsaki kamar malamai da sarakuna har ma da ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), wanda kuma akwai bukatar ganin gwamnatocin jihohi sun kara zage damtse wajen kaiwa ga cikakkiyar nasara”.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Daga bisani ya yaba wa Ministan ilimin ƙasar Dakta Tunji Alausa, da Ministar Kasa a ma’aikatar ilimi, Dakta Suwaiba Ahmed, shugaban hukumar Kula da ilimin Almajirai da yaran da basa zuwa makaranta ta Nijeriya, Dakta Mohammed Sani Idris, har ma jagororin addinai da sarakuna, bisa matakan da suke ɗauka na inganta ilimin Almajirai dama rayuwar yaran da basa zuwa makaranta ta hanyar koyar da su sana’oin hannu wanda zai basu damar dogaro da kansu, a ƙarƙashin shirin.

Allo
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
NAFDAC Ta Ƙona Kayayyaki Marasa Inganci Na Naira Biliyan 5 A Nasarawa

NAFDAC Ta Ƙona Kayayyaki Marasa Inganci Na Naira Biliyan 5 A Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.