ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za Mu Yi Hisabi Da Buhari A Gaban Allah — Sheikh El-Zakzaky

by Sadiq
9 months ago
Hisabi

Shugaban mabiya Shi’a a Nijeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya ce zai bari Allah Ya yi masa hukunci tsakaninsa da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, kan abin da ya faru da mambobin ƙungiyarsa a Zariya a shekarar 2015.

Rikicin ya fara ne lokacin da mambobin ƙungiyar suka tare wa tsohon Hafsan Soji, Laftanar Janar Tukur Buratai, hanya.

  • UNCTAD: Sin Na Daukaka Tsarin Cinikayya Tsakanin Bangarori Daban Daban Da Samar Da Tabbaci Ga Duniya
  • Ba Ni Da Shirin Komawa PRP – Gwamnan Bauchi

Abin da ya fara ne da rashin jituwa sannan ya rikiɗe zuwa babban rikici, inda sojoji suka buɗe wuta kan mabiyan ƙungiyar.

ADVERTISEMENT

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da rahoton kwamitin bincike na Jihar Kaduna sun tabbatar da cewa an kashe ɗaruruwan mambobin IMN kuma an binne su a asirce cikin daren da lamarin ya faru.

Daga baya an kama Sheikh Zakzaky da matarsa, aka tsare su har tsawon shekaru shida, kafin kotu ta wanke su a 2021.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

A yayin cika shekaru 10 da faruwar lamarin, Zakzaky, ya zargi gwamnatin Buhari da kin ɗaukar alhaki, duk da rahoton binciken da kwamitin ya kammala tun 2016.

Ya ce har yanzu gwamnatin yanzu ba ta ɗauki matakin da ta yi alƙawari ba, duk da cewa ta ce za ta biya iyalan waɗanda abin ya shafa diyya.

Ya ce: “Sun ce za su magance batun, amma shiru kake ji tun wancan lokacin.”

Da aka tambaye shi ko ya yafe wa Buhari, Zakzaky, ya ce ya bar komai a wajen Allah, kuma zai yi hisabi da shi a Ranar Alƙiyama.

Ya ce: “A ranar Alƙiyama za mu haɗu. Rayuwar Buhari ta ƙare.”

Zakzaky, ya ƙara da cewa harin da aka kai a 2015 bai karya ƙungiyarsu ta IMN ba, maimakon haka ya ƙara girman sunan ƙungiyar tare da yin fice a duniya.

Ya bayyana cewa sun kai ƙarar lamarin zuwa kotun ƙasa da ƙasa domin neman adalci, kuma a shirye suke su tattauna da gwamnati a ko da yaushe.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Neja Ta Miƙa Yara 100 Da Aka Ceto Ga Iyayensu

Gwamnatin Neja Ta Miƙa Yara 100 Da Aka Ceto Ga Iyayensu

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.