ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’ar MAU Ta Yaye Dalibai Dubu 5,545 A Yola

by Muh'd Shafi'u Saleh
2 years ago
Jami'ar

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, ya bukaci daliban da suka kammala karatu a jami’ar koyarwa ta Modibbo Adama da ke Yola (MAU), da su tashi tsaye da yin aiki tukuru, wajen tunkarar kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu da nan gaba.

Fintiri wanda mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta ta wakilta, ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a taron yaye daliban jami’ar karo na 28 ranar Asabar a Yola, ya ce jami’ar ta yi kokari na kyankyasa, da kuma yaye daliban da za su bayar da tallafin da kasa ke bukata.

  • Cutar Kyanda Ta Yi Ajalin Mutum 42 A Adamawa
  • Dan Majalisa Ya Kaddamar Da Ajujuwa 3 A Firamare A Adamawa

Ya ci gaba da cewa “dukkanmu mun taru ba kawai domin mu muku tafi kawai don kun samu nasara ba, amma sai don taya ku murna don samun kyakkyawar makoma mai dorewa,” in ji Fintiri.

ADVERTISEMENT

Haka kuma gwamna Ahmadu Fintiri, ya taya mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Liman, murnar kammala shekaru biyar na shugabancin jami’ar, ya kuma taya mataimakin shugaban jami’ar murnar shirya taron yaye dalibai sau uku a cikin shekaru biyar.

Da yake jawabin bude taron tunda farko shugaban jami’ar Sarkin Akwa Ibom Mai Martaba Okuku Uwa Umoh Adiaka na 3 kuma mai rike da sarautar karamar hukumar Obot Akara, ya taya daliban da aka yayen murna da nasarar da suka samu.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Haka shima mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Liman Tukur, ya amince da cewa ya cimma nasarorin ciyar da ci gaba da manufa da manufofin jami’ar ne da goyon baya, ya ce da ba zai samu ba idan bai samu hadin Kai da goyon baya ba.

Dalibai jimla dubu 5,545, suka kammala karatu a shekarar karatun ta 2022/3 a jami’ar, da suka hada da masu difloma 458, da 4,282 a fannin Digiri na farko, da zangon farko 53, zango na biyu 1,143 na sama, 2,376 a matakin kasa na biyu, zango uku 682 da digiri 28.

A bangaren digiri na farko, an kuma ba da takardar shaidar kammala digiri ga dalibai 41, masu digiri na biyu 630 da kuma Ph.D 134 a fannoni daban-daban.

Jami'ar
Muh'd Shafi'u Saleh
+ postsBio
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Jami’in Tsaro Ya Mayar da Dala 505 Da Riyal 30 Da Ya Tsinta A Yola
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Shahararren Malamin Addinin Islama A Adamawa Sheikh Ibrahim Abubakar Daware Ya Rasu
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    An Yi Wa ‘Yansanda 110 Ƙarin Girma A Adamawa
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Gwamna Fintiri Ya Nada Sabbin Sarakuna 7 A Jihar Adamawa

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
‘Yan Mata Mu Yi Karatu Sannan Mu Kama Sana’a – Khadija Sambo

‘Yan Mata Mu Yi Karatu Sannan Mu Kama Sana’a - Khadija Sambo

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.