ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Tarbiyya Da Ilimin Addini Ne Ke Sa Matasa Ɗaukar Doka a Hannu – Hon. Aminu Adam

by Shehu Yahaya
2 months ago
Addini

Ɗan takarar kujerar majalisar dokokin Jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, daga mazaɓar Kawo, Honarabul Aminu Adam, ya bayyana cewa ƙarancin ilimin addini da rashin tarbiyya na daga cikin manyan abubuwan da ke jefa wasu matasa cikin aikata munanan laifuka, ciki har da kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Honourable Aminu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron saukar karatun alƙurani na makarantar Jodan da ke Kaduna, inda ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun ƙaruwar matsalolin tsaro da kuma yadda wasu matasa ke ɗaukar doka a hannunsu ba tare da bin hanyoyin da doka ta tanada ba.

Ya ce, duk da cewa hukumomin tsaro na ci gaba da ƙoƙarin magance matsalar rashin tsaro, akwai buƙatar iyaye, malamai da shugabannin al’umma su taka rawar gani wajen tarbiyyantar da matasa tare da koya musu kyawawan ɗabi’u da darussan addini tun suna ƙanana.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, tarbiyya ita ce ginshiƙin zaman lafiya a kowace al’umma, kuma idan iyaye suka sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kula da tarbiyyar ƴaƴansu, za a rage yawan matasan da ke faɗawa cikin aikata laifuka da ɗaukar doka a hannu.

“Ya zama wajibi iyaye su sanya ido sosai kan halayen ƴaƴansu tare da tabbatar da suna samun ingantacciyar tarbiyya da ilimin addini. Idan aka yi haka, za a samu raguwar matsalolin da suka shafi tashin hankali da aikata laifuka,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Honourable Aminu ya ƙara da cewa ilimin addini yana koya wa mutum sanin darajar rayuwa, haƙurin zaman tare da mutunta doka, yana mai cewa duk matashin da aka gina bisa kyakkyawar tarbiyya ba zai kasance cikin masu aikata kisan gilla ko sauran miyagun ayyuka ba.

Ya yi kira ga gwamnati, malamai, ƙungiyoyin addini da na farar hula da su haɗa kai wajen wayar da kan matasa kan illolin tashin hankali, shaye-shaye da ɗaukar doka a hannu, domin samar da al’umma mai cike da zaman lafiya da haɗin kai.

Ɗan takarar ya jaddada cewa magance matsalar rashin tsaro aiki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa. Ya ce idan iyaye suka ba da muhimmanci ga tarbiyya da ilimin addini, al’umma za ta samu matasa nagari masu mutunta rayuwa da bin doka.

Addini
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.