ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Ƴan Nijeriya 2 A Afrika Ta Kudu

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da kisan wasu ‘yan Nijeriya biyu a Afrika ta Kudu, tare da buƙatar hukumomin ƙasar su gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa domin kamowa tare da hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin. Haka kuma, gwamnatin ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan Nijeriya da sauran baƙi da ke zaune a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, an bayyana mamatan da sunan Emeka Charles Iroegbu da Musa Yunana Joe, wanda aka fi sani da Big Joe. Sanarwar ta ce ana zargin jami’an ‘yansandan Tshwane Metro ne suka kashe Iroegbu a ranar 28 ga Yuni, 2026, a Sunnyside da ke Pretoria yayin wani bincike, yayin da Big Joe kuma wasu da ba a tantance ba suka harbe shi a gaban shagonsa da ke Witbank a lardin Mpumalanga.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta ce jami’an da ake zargi da kashe Iroegbu su ne kuma ake zargi da kashe wani ɗan Nijeriya, Nnaemeka Mathew Andrew Ekpenyong, a ranar 20 ga Afrilu, 2026, duk da cewa har yanzu ba a kama su ba. Ta kuma yi tir da kalaman wani jami’in gwamnatin Afrika ta Kudu da ya danganta ‘yan Nijeriya da safarar miyagun ƙwayoyi, tana mai cewa irin waɗannan kalamai na ƙarfafa ƙiyayya da hare-hare kan baƙi.

ADVERTISEMENT

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ‘yan Nijeriya da ke Afirka ta Kudu su kasance masu bin doka tare da gujewa wuraren da ke da haɗarin tashin hankali, yayin da ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya da kuma fitar da ‘yan Nijeriya da suka yi rajista daga ƙasar.

Ta kuma jaddada cewa Afirka ta Kudu na da alhakin kare rayuka da dukiyoyin baƙi, tare da gargaɗin cewa idan hare-haren suka ci gaba, Nijeriya za ta yi la’akari da ɗaukar wasu matakai.

LABARAI MASU NASABA

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa

MASU ALAKA

Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe
Manyan Labarai

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Labarai

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Next Post
Sin Da Rasha Za Su Gudanar Da Atisayen Sojojin Ruwa Da Sintiri Na Hadin Gwiwa

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.