Ƙungiyar likitoci masu koyon aiki ta ƙasa (NARD)ta sake ba Gwamnatin tarayya wa’adin mako huɗu waɗanda za ta yi amfani da su wajen maganin matsalolin da ƴan ƙungiyar suke fuskanta,da suke da alaƙa da jin daɗin su, da kuma matsalolin da mambobin su suke fuskanta a faɗin tarayyar Nijeriya, ya yin da ƙungiyar ta ke bayyana aniyar ta, ta tafiya yajin aiki idan gwamnatin ta ƙi biya masu buƙatunsu.
Matakin an ɗauke shi ne bayan da aka kammala wani taro na Shugabannin ta kafar sadarwa ta zamani ranar Asabar 27 ga Yuni, 2026, wannan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin na kwana 21- lokacin da ta yi babban taro.
A takardar da Shugaban ƙungiyar NARD, Dokta Mohammad Usman Suleiman,Sakatare Janar,Dokta. Shuaibu Ibrahim, Sakataren wayar da kan jama’a da jin daɗinsu, Dokta. Abdulmajid Yahya Ibrahim, kamar yadda ƙungiyar ta ce ta yi nazarin rahoton da aka samu daga wurin Shugabannin kwamitin ƙasa akan yadda ta kasance tsakninsu da hukumomi, da kuma aiwatar da abubuwan da aka amince ma wa.
Likitocin masu koyon aiki sun nuna rashin jin daɗinsu akan yadda gwamnatin tarayya ta kasa biyan kuɗaɗen horarwa na shekarar 2026 na su Likitoci masu koyon aikin bayan kuma duk an yi alkawarin cewar za a biya.
Hakanan ma sun nuna rashin jin daɗinsu akan ɓata lokacin da aka samu wajen rashin biyan albashi na Likitoci waɗanda basu daɗe da cancanta su yi aikin ba, su Likitoci ne ko kuma waɗanda suka karanta ɓangaren kula da haƙori, da wasu kuɗaɗen da suka kamata a basu, a wuraren da suke samun horo, kai har da ma da ci gaba da biyan kuɗaɗen da suka kamata amma ba a biya na kashi 25/35 CONMESS kan gyaran da aka yi na ariyas na watanni19 waɗanda suka shafi na ƙwararru.
Ƙungiyar ta ƙara nuna rashin jin daɗin ta dangane da ariyas na albashin da ƙarin girman da ba a biya ba, waɗanda Likitoci su ke bi a wuraren kuila da lafiya na faɗin tarayyar Nijeriya.
Hakanan ma NARD ta nuna yadda abin ya yi matuƙar damun ta akan irin rigingimun da ake ciki a Asibitin koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife (OAUTHC),inda suka ɗora alhakin abiunda ke faruwa ga Shugabanin wurin, wato yadda aka maida Likitoci masu koyon aiki saniyar ware,lamarin da suk ce yana shafar harkokin kula da lafiya da kuma horar da waɗanda suka kammala karatun na Likita da dai sauransu.
Ƙungiyar har ila yau ta yi tir da wani ƙoƙarin da su Shugabnnin na Asibitin koyarwar OAUTHC su fara shigo da maganar biyan wasu kuɗaɗe da ake kira da suna bench fees ga Likitoci masu koyon aiki waɗanda suke daga hukumomin kula da lafiya masu zaman kansu, duk kuwa da ya ke akwai wata takardar hana lamarin da gwamnati ta yi.
Ta wani ɓangaren kuma Bench fees (ko kuma “bench fees”)wasu kuɗaɗe ne da ake tilasta ko sa waɗanda suke yin kwas na digiri na biyu ko kuma na uku.Ana amsar su ne saboda lamarin da ya shafi bincike, kayan ɗakin bincike, kayan da za ayi hayar su, sai kuma horarwa ta musamman.
Su ma Shugabannin Asibitin koyarwa na Jami’ar Legas (LUTH) ba su tsira daga irin zargin ba domin kome ba sai saboda sun ƙi amincewa su samar da irin abincin da aka dafa a gida da kuma irin na gargajiya waɗanda za a iya kawo wa mutu a inda ya ke (call meals),wannan abin ya fi shafar Likitoci ma su koyon aiki duk kuwa da yake da akwai wani tsarin da aka yi dangane da hakan,bugu da ƙari kuma sun nuna ƙyama da irin abubuwan da ake yi waɗanda suka yi kama da na Legas da wasu Shugabannin Asibitocin koyarwar suke yi.
Hakanan ma ƙungiyar ta jinjinawa Jihohi da yawa da kuma hukumomin lafiya masu zaman kansu saboda yadda suka aiwatar da dukkan hakkoki na ma’aikatan lafiya, abin kuma ya kasance duk yadda yarjejeniyar ta kasance, kamar biyan ariyas na albashi, sai kuma ariyas na alawus ɗin da ya kamata a biya masu irin ƙwaraewar ta harkar lafiya, ba da kuɗaɗen da ake horar da waɗanda suka kamata a horar, da kuma samar da wata kafa ta jin daɗin Likitoci masu koyon aiki.
Ƙungiyar ta ce da akwai ci dangane da lamurran da suka shafi Hukumar daidaiton yadda ya dace a cɗauki ma’aikata.
A ƙarshen taron da aka yi ta kafar sadarwa ta zamani,an amince da a ƙara ba gwamnatin tarayya wa’adin mako huɗu domin ta samu damar aiwatar da duk ƙorafe-ƙorafensu, yayin da za a tattuna a taron kwamitin zartarwa zai yi a watan Yuli 2026 a Jihar Gombe.
NARD ta ja kunnen gwamnati cewar ba dole bane ta amince ta tsaya tana kallo ba kawa har idan bata ɗauki matakin da ya dace na biyan buƙatunsu ba, babu makawa sai sun tafi yajin aiki.
Ƙungiyar ta ce ma kwamitin Shugabannin ta na ƙasa da ya fara shirin tafiya yajin aiki, idan har gwamnati ta ƙi bin umarnin da ƙungiyar ta basu na mako huɗu ya wuce ba tayi kome ba.
Duk da yake ƙungiyar ta NARD ta amince da a zauna domin samun maslaha,duk da hakan ta ce tana iya ɗaukar matakin da ya kamata martsawar ba ayi mata maganin matsalolin da gwamnatin da ita suka amince ma wa ba, idan har ba a ɗauki matakin da ya dace ba.














