ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

by Rabi'at Sidi Bala
2 months ago
Ƴansandan

A wannna makon, za mu saurari ra’ayoyin masu karatunmu ne a kan shirin ƙirƙirro da ƴansanda jihohi da gwamnati ke shirin yi, wanda har majalisun ƙasa sun zartar da ƙudurin dokar, shin kuna ganin hakan zai kai ga kawo ƙarshen matsalolin tsaron da ake fuskanta a sassan ƙasar nan? Ga dai bayanan da muka samu, kamar yadda Sani Anwar ya tattara mana.

Umar Hussain Zam-zam, daga Jihar Kaduna

Mai fashin baƙi a kan harkokin yau da kullum a Jihar Kaduna, ya ce, “Samar da Ƴansandan jihohi, ba shi da wani alfanu a halin da muke ciki a ƙasar nan, dalili kuwa shi ne, kawai dai za a bai wa ƴan siyasa damar yin abin da suke so ne. Kar a manta fa, kwamishinan ƴansanda ba ya karɓar amsar umarni daga Sufeto Janar na ƴansandan Nijeriya, amma ka ga duk da haka ana samun matsala, ina kuma a ce sun koma ƙarƙashin gwamnonin jihohi. 

ADVERTISEMENT

Sunana Honarabul Sadiƙ Umar Ashafa, daga Jihar Kaduna 

Ɗan siyasa, kuma masanin harkokin tsaro a Jihar Kaduna, ya ce; samar da ƴansandan jihohi, akwai alfanu ta wata fuskar, kuma akwai tangarɗa a ɗaya fuskar. “Da farko dai, tsaro shi ne rayuwar Ɗan’adam, musamman ma talaka, wanda yanzu an samu matsala a kai. 

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

Samar da ƴansandan jihohi, zai taimaka wajen rage yawaitar ta’addanci, saboda zai taimaka wa jihohi wajen ganin an rage samun yawaitar matsalar tsaro.

“A Wani ɓangaren kuma, akwai yiwuwar gwamonin jihohi, za su riƙa amfani da ƴansanda, wajen yin abin da suke so, wanda kuma hakan bai kamata ba. Dama gwamnanoni suna ganin cewa; ba sa iya juya ƴansanda, waɗanda suke ƙarƙashin gwamnatin tarayya, ka ga yanzu idan aka samu ƴansandan jihohi, gwamnoni za su yi abin da suke so.

Sunana Usman Sani Amar, daga Abuja FCT

Tsaro na daga cikin manyan ginshiƙan ci gaban kowace ƙasa. A duk lokacin da rashin tsaro ya ƙaru, rayuwar al’umma da tattalin arziƙi sukan fuskanci barazana. Wannan ne ya sa batun kafa ƴansandan jihohi ya ci gaba da ɗaukar hankalin ƴan Nijeriya.

A ra’ayina, lokaci ya yi da ya kamata a yi nazari mai zurfi, kan kafa ƴansandan jihohi. Nijeriya ƙasa ce mai faɗin gaske, kuma yana da wuya rundunar ƴansandan tarayya kaɗai ta iya kula da harkokin tsaro yadda ya kamata a dukkan jihohin ƙasar.

Idan aka kafa ƴansandan jihohi, za su fi sanin al’adun yankunansu, yanayin muhalli da kuma mutanen da suke zaune a cikinsu. Wannan na iya taimakawa wajen gano masu aikata laifuka cikin sauri, tare da inganta tattara bayanan sirri da hana aikata laifi, tun kafin ya faru.

Sai dai kuma, akwai damuwar da ba za a yi watsi da ita ba. Wasu na tsoron cewa, gwamnonin jihohi na iya amfani da rundunar wajen cin zarafin masu adawa da su ko kuma nuna son kai wajen aiwatar da doka. Idan har ba a samar da ingantattun ƙa’idoji da tsarin sa ido mai zaman kansa ba, hakan na iya haifar da sabbin matsaloli, maimakon warware waɗanda ake fuskanta.

Sunana Bilkisu Maharazu, daga Jihar Katsina 

Kafa ƴansandan jihohi, na iya taimakawa wajen magance rashin tsaro. Abu na farko da nake son magana a kai shi ne, matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasarmu. Wannan matsala, ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi, tare da jefa al’umma cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali.

A ra’ayina, kafa ƴansandan jihohi na da matuƙar muhimmanci, idan har za a aiwatar da shi yadda ya kamata. Idan aka samar wa jami’an tsaro kayan aiki na zamani, aka ba su cikakken horo, aka biya su albashi mai kyau tare da inganta walwalarsu, kuma suka gudanar da aikinsu cikin gaskiya ba tare da cin hanci ko nuna son kai ba, ina da yaƙinin cewa; za a samu gagarumin ci gaba, wajen magance matsalar rashin tsaro.

Sunana Muhammad Idris Aliyu, CEO na Kamfanin

Sarkin Furniture International  

A zahirin gaskiya, kuma a ra’ayina, ba na goyon bayan lamarin ƴansadan jiha da gwamnati ke son ta ƙirƙiro, sakamakon su kansu waɗanda gwamnatin tarayya ta ɗauka, ba a biyansu buƙatunsu kamar yadda ya dace, ballantana a ce yanzu ma ƴansanda jihohi, ta ina za su fara? 

Ƴansanda abin girmamawa ne, sai dai kuma rashin kyakkyawan tsari a nan matsalar take, waɗanda ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya, babu wani tsari mai kyau da suke fuskanta, su ma da suka daɗe cikin yanayin kenan, to ina kuma ga waɗanda ba a ma ɗauke su ba, ballantana a fara ganin kamun ludayinsu, ko da ma an ƙirƙire su, daga ina ne za su fara? aikin fa ya yi wa Kurege yawa.

Sunana Muhammad Nura wanda aka fi sani da Daddy

A zahirin gaskiya, a ra’ayina ina goyon bayan ƴansandan jiha da majalisar dattawa ta amince da a ƙirƙiro da su, sakamkon yawan da aka yi har ayyukan tsaro sun yi wa waɗanda ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya yawa. Idan jihohi suna da nasu, kamar wani taimako ne suka yi wa gwamnatin tarayyar.

Bissalam, Allah ya ba mu zaman lafiya.

Sunana Umar Abdullahi, daga Jihar Zamfara 

Kafa ƴansandan jihohi na da amfani wajen inganta tsaro, idan aka tsara su da dokoki masu ƙarfi, musamman a wuraren Sakkwato, Kebbi, Katsina da ma Zamfara, inda muke fuskantar matsalar tsaro. Babu shakka, za su taimaka wa ƴansandan tarayya wajen kula da tsaro da kuma sanin yankin da al’adun mutanen jihar. Amma illolinta kuma su ne, gwamnoni na iya amfani da su wajen tsoratar da abokan adawa na siyasa da kuma cin zarafin haƙƙin Ɗan’adam, idan ba a sanya ingantattun dokoki ba.

Ƴansandan
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Next Post
An Gabatar Da Littafin “Bayanan Xi Jinping Kan Basirar Gudanar Da Ayyuka A Kananan Hukumomi”

An Gabatar Da Littafin “Bayanan Xi Jinping Kan Basirar Gudanar Da Ayyuka A Kananan Hukumomi”

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.