Babban jirgin sama samfurin AG600 mai suna Kunlong da Sin ta kera a cikin gida, wanda ke iya tashi da sauka a kan doron kasa da cikin ruwa, ya kammala aikinsa na bana a Jiagedaqi da ke lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin.
Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin wato AVIC ya bayyana a yau Litinin cewa, jirgin ya yi nasarar kammala ayyukan kai daukin gaggawa da na kare gobarar daji, na tsawon watanni 4 a sararin samaniya.
Kuma yayin aikin na watanni 4, ya yi tafiye-tafiye domin sintiri sau 35, inda ya kwashe tsawon sa’o’i 100 na tafiya lami lafiya, ya kuma zubo da ruwa kimanin ton 390.
Bisa la’akari da yadda yake iya shawagi a kusa da doron kasa kuma ba tare da gudu sosai ba, da karfinsa na daukar ruwa mai yawa da saukin sauya alkibla, jirgin ya nuna karfinsa na kai daukin gaggawa da kashe gobara a dazuka masu sarkakiya.
Kasar Sin ce ta kera jirgin na Kunlong da kanta, domin biyan bukatun kasar na kashe gobarar daji da ayyukan ceto a cikin ruwa. Kuma shi ne irinsa mafi girma a duniya da ba na aikin soja ba, idan aka kwatanta da nauyin da yake iya tashi da shi.
Nan gaba, jirgin zai shiga matakin aiki na yau da kullum, inda zai taimaka wa wani sabon samfuri mai karewa da kashe gobarar daji. (Fa’iza Mustapha)














