Babban Darakta kuma shugaban hukumar tsara wa da bunƙasa ƙera Motoci na ƙasa (NADDC), Otunba Oluwemimo Joseph Osanipin, ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnati ta ba wa kamfanoni 81 lasisin sayar da iskar gas na motoci (CNG) a faɗin Nijeriya.
Osanipin ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, jim kaɗan bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu. Ya ce samun ƙarin waɗannan kamfanoni, wanda a baya guda huɗu ne kacal, na nuni da irin ci gaban da ƙasar ke samu wajen bunƙasa tsarin nan na Gwamnatin Tarayya domin a samu wadatar iskar gas ɗin a sassan ƙasar nan.
Shugaban na NADDC ya jaddada cewa aiwatar da irin wannan tsari yana buƙatar gagarumin zuba jari a gidajen mai, da tsarin raba iskar gas na tafi-da-gidanka, da kuma wuraren sarrafa shi kafin a fara ganin tasirinsa gadan-gadan. Ya ce, “Ba za ka ƙirƙiro tsari a yau ba, kuma ka fara ganin tasirinsa nan take ba.” Don nuna amfanin tsarin, Osanipin ya ba da misali da wani matafiyi da ya je Jigawa da Kano wanda ya samu nasarar rage kuɗin da yake kashewa a man fetur daga sama da Naira 200,000 zuwa kusan Naira 40,000 bayan ya sha gas ɗin CNG a Kano.
Duk da wannan gagarumin sauki, Osanipin ya koka kan yadda masu kamfanonin safarar ababen hawa da ke cin gajiyar tsarin CNG suka ƙi rage kuɗin sufuri don talakawa su amfana, inda ya ce hakan shi ne “mataki na gaba” da za a tunkara. Sai dai ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta fara tabbatar da cewa an samar da isassun ababen more rayuwa kafin a fara tsaurara dokokin dake ƙarfafa amfani da iskar gas ɗin a faɗin ƙasar nan don samun makamashi mai tsafta.
Kan batun motoci masu amfani da wutar lantarki (EVs), Osanipin ya ce tuni an samar da wuraren cajin motocin a kusan jami’o’i 16 a matsayin wani ɓangare na tallafawa yaduwar fasahar.
Har ila yau, ya sanar da cewa an riga an miƙa kashin farko na motocin lantarki da Shugaba Tinubu ya yi alƙawarinsu ga ma’aikatan gwamnati, yana mai cewa, “wannan shi ne farkon abubuwa da yawa da za su zo” wajen sauya fasalin sufuri zuwa mai tsafta kuma mai matuƙar sauƙin kuɗi a Nijeriya.














