ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin: Yana Da Muhimmanci A Sabunta Ka’idoji Da Matakin Karshe Na Shari’o’in Tokyo

by Sulaiman
4 months ago

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, bisa la’akari da karuwar farfado da karfin soja a Japan da zama barazana ta hakika, abu ne mai muhimmanci a sabunta ka’idoji da matakin karshe na shari’o’in Tokyo watau Tokyo Trials.

Kakakin ya ce, a ranar 3 ga watan Mayun shekarar 1946, biyo bayan tanade-tanaden mika wuya da Japan ta yi ba tare da wani sharadi ba da kuma na kotun hukunta laifukan yakin duniya na II da kasashen kawance suka gabatar, kotun ta fara sauraron shari’a kan laifukan yakin, kuma bisa haduwar manyan kasashe 11 da hujjoji da shaidu masu karfi da aka gabatar, wadannan shari’o’i sun samu sojojin Japan da laifin kaddamar da yaki da take dokokin kasa da kasa da bayyana irin ta’asar da Japanawa suka aika a kasashen Asiya da dama.

An kuma yankewa manyan masu laifi su 25 hukuncin kisa ta hanyar rataya ko zaman gida yari, cikinsu har da Hideki Tojo. Haka kuma an karyata shari’o’i kamar “shari’ar tabbatar da nasara” da “yakin Japan na kare kai” da “dokar gyara hukunce-hukunce.”

ADVERTISEMENT

A cewar kakakin, shari’o’in na Tokyo, wanda gwaji ne na sanin ya kamata, ya tabbatar da adalci a tarihi. Kuma idan aka hada da shari’o’in Nuremberg, shari’o’in na Tokyo sun kunyata masu ra’ayin danniya da suka aikata laifukan yaki.

Ya ce bai kamata a yi watsi da adalcin da shari’o’in biyu suka tabbatar ba. Haka kuma bai kamata a kalubalanci ikon da suke da shi bisa doka ba. Kuma bai kamata a jirgita odar duniya da suka shimfida bayan yakin ba.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Bugu da kari, ya ce duk yunkurin wani na yin gangancin gyara hukuncin da aka yanke, zai fuskanci turjiyar jama’ar duniya masu kaunar zaman lafiya, tare da sake gurfana gaban kotu. (Fa’iza Mustapha)

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

MASU ALAKA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Next Post
APC Ta Amince Da Dr. Jamilu Shaiyaku A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe

Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.