ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Yadda Aka Hallaka Malamar Islamiyya A Kaduna

by Sulaiman and Shehu Yahaya
2 months ago
Malama

Wani mummunan al’amari da ya girgiza zukatan al’umma ya faru a yankin Maraban Jos da ke ƙaramar hukumar Igabi a Jihar Kaduna, inda wata malamar Islamiyya, Ummulkhairi, ta rasa ranta bayan wasu fusatattun matasa sun zarge ta da satar yara ba tare da gabatar da wata hujja da ta tabbatar da hakan ba.

Lamarin, wanda ya haifar da ɗimbin ce-ce-ku-ce da alhini a cikin al’umma, ya sake jawo hankali kan haɗarin yaɗa jita-jita da kuma ɗaukar doka a hannu, wani abu da masana da masu fafutukar kare haƙƙin Ɗan’adam ke ganin yana ƙara zama barazana ga zaman lafiya da adalci.

Duk da ƙoƙarin wasu mutane na ceto ta, lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali wanda ya yi sanadiyyar rasa ranta. Al’ummar yankin da ƙungiyoyi daban-daban sun yi Allah-wadai da kisan tare da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gurfanar da masu hannu a wannan aika-aika.

ADVERTISEMENT

Marigayiyar ta bar gidanta a Sabon Garin Maraban Jos ne domin halartar wata muhadara da malamai suka shirya a makarantar Tashiyhul Iman da ke tsohuwar Maraba.

A cewar shaidun gani da ido, bayan abokan tafiyarta sun riga sun wuce gaba, sai ta tsaya tambayar hanyar zuwa wurin taron.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

 Ana zargin cewa yayin da take tambayar wasu yara hanyar, wasu mutane suka yi mata kallon shakku tare da fara yaɗa zargin cewa mai satar yara ce.

Cikin ƙanƙanin lokaci, jita-jitar ta bazu kamar wutar daji, lamarin da ya sa jama’a suka fara taruwa a kanta cikin fushi da zargi.

Da tashin hankalin ya fara ƙamari, jami’an tsaro sun kai Ummulkhairi ofishin ƴansanda domin kare lafiyarta tare da gudanar da bincike kan zargin da ake yi mata.

Shaidu sun shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa a lokacin da take hannun jami’an tsaro, wakilan iyalanta da wasu daga cikin danginta sun isa ofishin domin tabbatar da asalinta. Sun bayyana cewa fitacciyar malamar addini ce mai koyar da yara da mata ilimin addinin Musulunci, kuma babu wata hujja da ke nuna cewa ta aikata laifin da ake zarginta da shi.

Sai dai duk da wannan bayani da ƙoƙarin wasu masu ruwa da tsaki na kwantar da tarzoma, fushin wasu matasa bai lafa ba.

Shaidu sun bayyana cewa daga bisani lamarin ya rikice ya koma rikici, inda fusatattun matasa suka afka wa malamar.

Wani matasa mai suna Ukasha Umar wanda abin ya faru gabansa ya shaida wa wakilinmu cewa

 an yi mata dukan tsiya kafin daga bisani aka kashe ta tare da ƙona gawarta, abin da ya jefa iyalai, abokai, ɗalibai da ma al’ummar yankin cikin matsanancin jimami.

Ba ita kaɗai ba ce ta gamu da wannan iftila’i. Rahotanni sun kuma nuna cewa an ƙone babur ɗin wani malami da ya yi ƙoƙarin shiga tsakani domin cetonta daga hannun masu harin.

Bayan aukuwar lamarin, wasu bayanai da suka bazu a kafafen sada zumunta sun yi zargin cewa jami’an ƴansanda ne suka miƙa matar ga fusatattun matasa.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ƴansandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya musanta wannan zargi.

A wata tattaunawa da manema labarai, ya ce jami’an tsaro sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen kare rayuwar marigayiyar, kuma su ne suka fara cetonta daga hannun jama’a tun da farko.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan yankin ma sun yi iya ƙoƙarinsu wajen hana aukuwar lamarin, amma lamarin ya fi ƙarfin yadda ake zato.

Biyo bayan kisan gillar, gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci.

Shugaban ƙaramar hukumar Igabi, Sani Abdul, wanda ya ziyarci iyalan marigayiyar ya tabbatar da cewa gwamnati ta shiga cikin lamarin tare da bibiyar yadda abin ya faru wanda kuma za ta ɗauki matakan da suka kamata wajen daƙile yaɗuwar duk wata fitana.

Haka kuma, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu, ta jajanta wa iyalan marigayiyar tare da bayyana cewa gwamnati za ta tallafa musu a wannan lokaci na jimami.

Ta ce mutuwar Ummulkhairi ba kawai rasa rai ba ce, wani abin tunatarwa ne ga al’umma kan illar yanke hukunci bisa jita-jita da zarge-zarge marasa tushe.

Malama
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Malama
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Ziyarci Iyalan Malamar Addini Da Aka Kashe A Kaduna Saboda Zargin Satar Yara

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.