ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Uba Sani Ya Ziyarci Iyalan Malamar Addini Da Aka Kashe A Kaduna Saboda Zargin Satar Yara

by Sulaiman
3 weeks ago
Uba sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayiya Ummulkhairi Usman Aliyu, wadda wasu fusatattun mutane suka kashe bisa zargin satar yara a yankin Maraban Jos da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook bayan ziyarar da ya kai wa iyalan marigayiyar a ranar Asabar da yamma domin jajanta musu da kuma nuna goyon bayan gwamnati a wannan lokaci na tsananin baƙin ciki.

A cewarsa, gwamnatin jihar za ta tabbatar an gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda ke da hannu a kisan a gaban kotu domin a hukunta su bisa doka.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, Gwamna Sani ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin ilimi da walwalar ‘ya’yan marigayiyar domin rage wa iyalanta radadin rashin da suka yi.

Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar, wacce malamar addinin Musulunci ce, ta ɓata hanya ne yayin da take kan hanyarta ta zuwa wani taro a ranar 21 ga Yuni, 2026, kafin wasu mutane su zarge ta da satar yara. Duk da cewa tana hannun jami’an tsaro a Maraban Jos, amma an ƙwace ta daga wurinsu sannan aka yi mata dukan tsiya har ta rasa ranta.

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

Lamarin ya haifar da damuwa da kira daga al’umma da kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama kan buƙatar dakile hukuncin daukar doka a hannu da tabbatar da cewa ana barin hukumomin tsaro da kotuna su gudanar da aikinsu bisa doka.

Uba sani
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya
  • Sulaiman
    Omar M. Yaghi: Kalaman Xi Sun Kara Mana Kwarin Gwiwa
  • Sulaiman
    Manufar Sin Ta Ba Da Jagoranci Ga Tafiyar Da Fasahar AI A Duniya
  • Sulaiman
    CDC Ta Afirka Ta Yaba Wa Sin Bisa Goyon Bayanta Ga Dakile Cutar Ebola

MASU ALAKA

Majalisa Ta Goyi Bayan CBN Kan Sauya Fasalin Naira Bayan Tafka Muhawara 
Labarai

Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo

July 18, 2026
Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna
Rahotonni

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

July 18, 2026
Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Kama Mutum 10 Kan Kisan Shugaban MACBAN Na Jihar Binuwe

Ƴansanda Sun Kama Mutum 10 Kan Kisan Shugaban MACBAN Na Jihar Binuwe

LABARAI MASU NASABA

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

July 18, 2026
Xavi Ya Ce A Shirye Yake Ya Karɓi Ragamar Horar Da Tawagar Ƙasa

Xavi Ya Ce A Shirye Yake Ya Karɓi Ragamar Horar Da Tawagar Ƙasa

July 18, 2026
Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya

Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya

July 18, 2026
Burina Zama Daya Daga Cikin Fitattun Masu Daukar Hoto A Nijeriya –Ibrahim Aminu

Burina Zama Daya Daga Cikin Fitattun Masu Daukar Hoto A Nijeriya –Ibrahim Aminu

July 18, 2026
Omar M. Yaghi: Kalaman Xi Sun Kara Mana Kwarin Gwiwa

Omar M. Yaghi: Kalaman Xi Sun Kara Mana Kwarin Gwiwa

July 18, 2026
Manufar Sin Ta Ba Da Jagoranci Ga Tafiyar Da Fasahar AI A Duniya

Manufar Sin Ta Ba Da Jagoranci Ga Tafiyar Da Fasahar AI A Duniya

July 18, 2026
CDC Ta Afirka Ta Yaba Wa Sin Bisa Goyon Bayanta Ga Dakile Cutar Ebola

CDC Ta Afirka Ta Yaba Wa Sin Bisa Goyon Bayanta Ga Dakile Cutar Ebola

July 18, 2026
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta

July 18, 2026
Xi Jinping Ya Bukaci A Gudanar Da Aikin Ceto A Tsanake Bayan Rugujewar Bangaren Wani Tsauni A Chongqing

Xi Jinping Ya Bukaci A Gudanar Da Aikin Ceto A Tsanake Bayan Rugujewar Bangaren Wani Tsauni A Chongqing

July 18, 2026
Yadda Ake Miyar Karkashi Da Nama

Yadda Ake Miyar Karkashi Da Nama

July 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.