ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Lakaɗawa Wata Malamar Makaranta Duka Har Lahira A Lokoja

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Rundunar Ƴansandan Jihar Kogi ta ƙaddamar da bincike mai zurfi kan kisan gillar da aka yi wa wata malama, Maryam Usman, wadda aka yi wa duka har lahira a garin Lokoja. Wannan mummunan lamari ya auku ne bayan da malamar, wadda ke koyarwa a makarantar “Muslim Community Nursery and Primary School”, ta ladabtar da wani ɗalibi saboda saɓa dokar makaranta, lamarin da ya sa ɗalibin ya tafi gida ya kira danginsa domin su ɗauki fansa.

Daily Trust ta bayyana cewa mahaifiyar ɗalibin tare da yayyensa maza sun biyo malamar har gidanta da ke unguwar Sarkin Noma a Lokoja, inda suka far mata da duka da itace ba kaukauta. Suka yi mata dukan tsiya a gaban mutane har sai da ta suma, inda daga baya aka garzaya da ita asibiti amma aka tabbatar da cewa ta rasu sakamakon raunin da ta samu a kanta.

Wannan ɗanyen aiki ya tayar da hankulan mazauna garin Lokoja da ɗaukacin ƙungiyoyin malamai na jihar, waɗanda suka fito fili suka yi Allah-wadai da kisan tare da neman gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa na kare rayukan malamai. Iyalin marigayiyar Maryam Usman da shugabannin al’umma sun yi kiran da a gaggauta kamo waɗanda suka aikata wannan kisa domin yi wa malamar adalci.

ADVERTISEMENT

Kakakin rundunar ƴansandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro suna can suna farautar mutanen da suka aikata kisan waɗanda tuni suka tsere bayan sun gama tafka wannan ta’asa.

Rundunar ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci irin wannan ɗaukar doka a hannu ba, kuma za a gurfanar da duk wanda aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukuncin kisan kai.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna

MASU ALAKA

Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe
Manyan Labarai

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
Shigo Da Fetur Daga Waje Ya Sauka Zuwa N983.92, Ya Fi Na Matatar Dangote Arha

Shigo Da Fetur Daga Waje Ya Sauka Zuwa N983.92, Ya Fi Na Matatar Dangote Arha

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.