Adadin mutanen da suka mutu a harin da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Kankara da ke a Jihar Katsina ya karu zuwa 102.
Daga cikin wadanda aka kashe akwai ‘yan aikin-sa -kai da suka fito daga kauyukan Guga, Kakumi, Kandarawa da Jargaba da ke a Karamar Hukumar Bakori, inda a nan ne ayyukan ‘yan bindigar ya fi munana.
- Wani Ya Kashe Dan Uwansa Kan Naira 1,000 A Jihar Legas
- An Gurfanar Da ‘Yan Bangar Siyasa 10 A Gaban Kotu A Sakkwato
Wani shugaban al’umma a kauyen Guga Mahadi Guga ya sheda wa Leadership Hausa cewa, sun birne gawarwarki guda 72 da aka kwaso daga daji, inda ya kara da cewa, mutane guda 102 ne ‘yan bindigar suka kashe.
Mahadi, ya kara da cewa, mutane 102 aka hallaka, mun kuma mun birne mutane 72, inda kuma har yanzu, akwai mutanen da ba a gansu ba har yanzu.
A cewarsa, har yanzu muna cikin zaman dar-dar tun bayan aukuwar harin, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta sauke nauyin da ke a kanta na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar, musamman wadanda ke zaune a karkara.
Tun bayan aukuwar harin, rundunar ‘yansandan jihar, ta tabbatar da cewa, mutane 41 ne suka mutu a lokacin harin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp