Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani mutum mai suna Ayuba Sani Tumfafi hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan gyaran hali, bayan samunsa da laifin kashe abokinsa, Ibrahim Dan Larai, sakamakon wata sa-in-sa da ta ɓarke a tsakaninsu kan batun tashi domin gudanar da sallar Asuba. Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, wadda ta jagoranci shari’ar a Babbar Kotu Mai Lamba 1, ita ce ta yanke wannan hukunci a Kano a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 2026.
Bayanai a gaban kotun sun nuna cewa rikici ya ɓarke ne tsakanin Tumfafi da marigayin bayan sun samu saɓani kan batun tashi zuwa sallar asuba, lamarin da ya rikiɗe zuwa faɗa da ya yi sanadin mutuwar Ibrahim. A yayin shari’ar, lauyar masu shigar da ƙara, Amina Uba Adamu, ta gabatar da shaidu uku da kuma hujjoji guda uku domin tabbatar da zargin kisan da ba na ganganci ba, yayin da wanda ake tuhumar kuma ya kare kansa a gaban kotun.
Bayan kammala sauraron hujjoji da shaidun kowane ɓangare, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ta bayyana cewa an sami Tumfafi da laifin kisan ba tare da haƙƙi ba, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari.
Baya ga hukuncin ɗaurin, kotun ta kuma umarci wanda aka yanke wa hukuncin da ya duƙufa wajen neman ilimin addinin Musulunci da na zamani a tsawon lokacin da zai kwashe yana zaman kaso a gidan gyaran halin, domin zama tubalin gyaruwar halayensa kafin cikar wa’adinsa.














