Babbar Kotun jihar Sokoto ta yankewa mambobin rundunar sa- kai ta Civilian Joint Task Force (CJTF) guda uku hukuncin kisa ta hanyar rataya a bisa laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, da fashi da makami da kuma kisan kai.
Waɗanda kotun ta kama da laifin tare da yankewa hukuncin su ne; Gaji Hassan, da Abdullahi Goni Gudusu da Modu Bukar a ranar Alhamis a ƙarƙashin Mai Shari’a Kabiru Muhammad. A sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na kotun, Nakwanta Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewar laifin da suka aikata ya faru ne a ranar 19 ga Satumba 2024 da misalin karfe 4:30 na yamma a ƙauyen Kagara da ke Karamar Hukumar Goronyo a jihar Sakkwato.
Kotun ta bayyana cewar waɗanda ake tuhumar sun ɗauke bingida sun tare Babangida Nasiru da wata mata sannan suka tafi da su cikin daji suka karɓi naira dubu 260, 000 a hannun su kuma daga baya aka gano gawar Nasiru da raunukan harbin bindiga a kirji da wuyansa.
Kotun ta bayyana cewar waɗanda suka shigar da ƙarar sun gabatar da shaidu biyu da sahihan hujjoji waɗanda kotu ta gamsu da su kuma waɗanda ake ƙarar sun kasa kare kan su. Alƙalin ya ce shaidar mutun daya da ya tsira daga lamarin kadai ta isa ta tabbatar da laifin waɗanda ake tuhuma.
A yayin zartas da da hukuncin, alƙalin ya bayyana cewar a bisa ga tanadin kundin dokar penal code ta jihar Sakkwato ta 2019, ta ɗaure kowane daya daga cikin mutanen uku hukuncin kisa ta hanyar rataya amma suna da damar ɗaukaka ƙara a cikin kwanaki 90.














