Majalisar Sarkin Musulmi ta bayyana cewar ta yi nisa a shirin kafa karamin bankin musulunci domin yaki da talauci, samar da ayyukan yi da inganta hanyoyin dogaro da kai a fadin kasa da kasashen yankin Yammacin Afurka.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Sakkwato a yayin bude taron horaswa ga masu ruwa da tsaki kan tsarin Baitul Mal- wat Tamweel (BMT)Bankin Raya Ƙasashen Musulunci ne ya shirya taron tare da hadin guiwar Hukumar Zakka da Wakafi ta jihar Sakkwato.
Sarkin Musulmin wanda Uban Kasar Kilgori, Dakta Muhammad Jabbi Kilgo ya wakilta, ya bayyana cewar bankin zai baiwa kananan ’yan kasuwa damar samun kudaden gudanar da kasuwanci bisa tsarin kudi na musulunci domin fadada harkokinsu, samar da ayyukan yi da inganta rayuwarsu.
Ya ce shirin ya yi nisa sosai wanda masu zuba jari, ciki har da wadanda ke wajen Nijeriya suka nuna sha’awar hada guiwa wajen tabbatar da kafuwar bankin. Sarkin Musulmi ya jaddada cewar manufar kokarin da suke yi shine kafa bankin da zai zama abin koyi, ba wai ga Nijeriya kadai ba, har ma ga kasashen yankin Yammacin Afurka.














