ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Tattalin Arziƙi Ta Ƙasa (NEC) Ta Amince Da Tsarin Kwana 90 Na Rage Tsadar Rayuwa

by Abubakar Sulaiman
10 hours ago
Rayuwa

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (National Economic Council — NEC) ta amince da wani shirin gaggawa na kwanaki 90 da ke da nufin rage raɗaɗin tsadar rayuwa, da sauƙaƙa farashin kayan abinci, da kuma jawo masu zuba jari a faɗin Nijeriya. Wannan mataki ya samu amincewa ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 2026, yayin taron majalisar karo na 161 wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta ta hanyar bidiyo.

Shirin, wanda Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta tsara, ya ta’allaƙa ne a kan muhimman batutuwa guda biyar: sauƙaƙa farashin abinci, da daidaita tsarin karɓar haraji, da kammala manyan ayyukan da suka fi amfanar talakawa, da kawar da cikas ga masu zuba jari, da kuma tsara ingantaccen tallafi ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi. Bugu da ƙari, majalisar ta amince da kafa wata kafa ta musamman ta intanet (national dashboard) domin bibiyar ayyukan ƙasa tare da fayyace yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka tara sakamakon janye tallafin man fetur cikin gaskiya da riƙon amana.

A jawabinsa, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya buƙaci gwamnonin jihohi da hukumomin gwamnati da su tabbatar da cewa alfanun sauye-sauyen tattalin arziƙin Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne rage kuɗin sufuri, da inganta kiwon lafiya, da samar da ayyukan yi.

ADVERTISEMENT

Dangane da fannin sufuri, Shettima ya jaddada cewa ya kamata a auna nasarar shirin motocin bas masu amfani da iskar gas (CNG) ta hanyar sauƙaƙa kuɗin mota ga fasinjoji maimakon yawan motocin da aka raba, inda aka amince da tsarin haɗin gwiwar kuɗi tsakanin tarayya da jihohi don bunƙasa motocin CNG da masua amfani da wutar lantarki.

Rayuwa
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
  • Abubakar Sulaiman
    Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
  • Abubakar Sulaiman
    Aikin Titin Jirgin Ƙasa Na Kaduna Zuwa Kano Ya Kai Kashi 90%

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau
Manyan Labarai

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Next Post
TCN Ta Buɗe Sabbin Tashoshi 4, Wutar Lantarkin Kano Ta Ƙaru Da 544MW

TCN Ta Buɗe Sabbin Tashoshi 4, Wutar Lantarkin Kano Ta Ƙaru Da 544MW

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.