ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Yadda Gwamnatin APC Ke Farautar Ƴan Adawa

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
2 weeks ago
Gwamnatin

Watanni uku gabanin zaɓen 2027, jagororin jam’iyyun adawa a Nijeriya na ci gaba da fuskantar matsin lamba a farautar da jam’iyya mai mulki ke yi musu a ƙoƙarin karya lagonsu kamar yadda suka bayyana.

Jagororin jam’iyyar adawa ta ADC sun bayyana cewa ƙoƙarin binciken Atiku Abubakar, da binciken da ake yi wa tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai wanda ke tsare na tsawon watanni, da tsohon Ministan Shari’a kuma ɗan takarar Gwamna na ADC a Jihar Kebbi Abubakar Malami, da tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal da sauransu, a matsayin misalan yadda jam’iyya mai mulki ke farautar abokan hamayya.

Haka ma bayanai sun nuna a yanzu haka jam’iyya mai mulki na aiwatar da wani shiri na musamman na sayen ƴan takarar jam’iyyun adawa domin su janye takararsu tare da samun tukucin tsabar kuɗi: daga Naira miliyan 50 ga ƴan takarar majalisar jiha, da Naira miliyan 200 ga ƴan takarar majalisar wakilai, Naira miliyan 500 ga ƴan takarar majalisar dattawa, zuwa Naira biliyan biyu ga ƴan takarar gwamna.

ADVERTISEMENT

Zargin, wanda jigo a jam’iyyar NDC Buba Galadima ya bayyana a hirarsa da gidan talabijin na Arise, ya nuna cewa tuni ƴan takara da dama suka sanya hannu kan janye takararsu tare da karɓar kuɗaɗe da motoci. Ya kuma ce wata mata ce daga Jihar Zamfara ke bayar da kuɗaɗen a Abuja a madadin jam’iyyar ƙarƙashin sa idon jami’an tsaro.

Haddasa rikice-rikicen cikin gida a mabambantan jam’iyyu, da ƙaƙaba shari’u daban-daban a kotuna, da sauya sheƙar jigogin siyasa, da binciken hukumomin yaƙi da cin hanci na EFCC da ICPC kaɗan ne daga cikin farautar da jam’iyya mai mulki ke yi wa ƴan adawa.

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

Tuni dai jam’iyyun adawa suka zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunƙurin yi musu kisan mummuƙe da manufar mayar da siyasar Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya tilo, zargin da wasu suka ce akwai ƙamshin gaskiya a cikinsa, duba da irin wutar da ke ci gaba da ruruwa a jam’iyyun adawa.

Masu wannan ra’ayin sun danganta hakan ne da yadda manyan jiga-jigan ƴan siyasa, ciki har da gwamnoni da ƴan majalisun tarayya, suka riƙa rububin komawa APC, abin da suke ganin zai rage ƙarfin fafatawar zaɓen da ke tafe.

Rashin ba wa jam’iyyun adawa cikakkiyar damar auna tsawonsu da jam’iyyar APC mai mulkin ƙasa babbar barazana ce ga mulkin dimokuraɗiyyar Nijeriya, kamar yadda masu ruwa da tsaki a siyasar ƙasar suka bayyana tare da yin kakkausan gargaɗi a kai.

Jam’iyyun adawa sun zargi hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da yin amfani da bincike wajen matsa musu lamba domin su shiga jam’iyya mai mulki ko kuma su jingine duk wata fafutuka ta adawa, zargin da jam’iyyar APC ta yi watsi da shi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya soki yadda gwamnatin Tinubu ke mayar da hankali kan durƙusar da ƴan adawa maimakon magance manyan matsalolin da ke addabar ƙasar, kama daga taɓarɓarewar tsaro, da matsin tattalin arziƙi, da talauci, zuwa rashin aikin yi, yana mai cewa ko kaɗan hakan ba shugabanci ba ne.

Ya ce, “Ƴan Nijeriya na ganin abin da ke faruwa. Ana kai hari ga jam’iyyun adawa, ana matsawa jam’iyyun siyasa lamba, kuma ana amfani da ƙarfin ikon gwamnati ba don ci gaban ƙasa ba, sai dai domin kare muradun siyasa.”

A kan wannan ya yi gargaɗin cewa idan ba a gyara wannan gurɓataccen yanayin ba, hakan zai sa jama’a su dawo daga rakiyar mulkin dimokuraɗiyya, domin an tauye damar da ƴan ƙasa suke da ita ta zaɓen jam’iyyu da ƴan takarar da suke ra’ayi a 2027.

A cewar Atiku, binciken abokan adawa da ake yi alama ce da ke nuna cewa ana ƙoƙarin karya lagon jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027, lamarin da ya ce zai iya rage zafin gwagwarmaya a zaɓen tare da hana jama’a zaɓen waɗanda suke so.

Atiku ya bayyana cewa a fili yake gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali ne kacokam wajen kawar da manyan abokan hamayya gabanin zaɓen 2027 ta hanyar raunata su, yana mai gargaɗin cewa hakan na iya zama babbar barazana ga makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Jam’iyyar adawa ta ADC ita ce kan gaba wajen fuskantar ƙalubale, musamman biyo bayan hukuncin soke rajistar jam’iyyar da kotu ta yanke, wanda ya janyo cece-kuce a tsakanin ƴan siyasa, da magoya baya, da lauyoyi, da masana harkokin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Dakatar da ƙoƙarin soke rajistar jam’iyyun adawa na ɗaya daga cikin dabarun kawar da abokan hamayya a akwatin zaɓen 2027; hukuncin Kotun Ƙoli na yin watsi da batun soke jam’iyyun wani mataki ne na ceto dimokuraɗiyya daga rushewa.

Duk da dai ADC da sauran jam’iyyu sun samu nasara a Kotun Ƙoli, wadda ta bayar da umarnin a ci gaba da sauraren shari’ar a Kotun Ɗaukaka Ƙara, babu tabbacin abin da zai biyo baya. Sauran jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da Action Peoples Party, da Action Alliance, da Accord Party, da kuma Zenith da Labour Party, waɗanda duka kotun ta ce ba su cika ƙa’idojin da ake buƙata ba a matsayin jam’iyyun siyasa.

Jim kaɗan da kafuwarta, jam’iyyar ADC ta shiga matsalolin cikin gida da suka shafi shugabanci har ta kai ga shari’u kan halaccin zaɓukan cikin gida, lamarin da ya rage mata ƙarfi tare da jawo sauya sheƙar wasu jigogi da kuma rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobinta.

Haka ma masu fashin baƙin siyasa na ganin akwai sa-hannun gwamnati wajen kawo cikas ga ƙoƙarin haɗa kan ƴan adawa a ƙarƙashin wata babbar jam’iyyar haɗaka, sakamakon saɓani da ya kunno kai a tsakanin manyan ƴan siyasa, wanda ya hana kafa ƙwaƙƙwarar jam’iyyar da za ta iya zama babbar barazana ga APC a akwatin zaɓe.

A gefe guda, jam’iyyar PDP, wadda a baya ke jan ragamar mulki kafin ta zama jam’iyyar adawa, ta fuskanci zazzafan rikicin shugabanci da ya ƙasƙantar da ita tare da raba kan jam’iyyar gida biyu, ta yadda kowane ɓangare ke iƙirarin shi ne sahihi.

Rikicin jam’iyyar PDP ya zama silar shari’u daban-daban a kotuna da kuma kafa kwamitoci masu cin karo da juna, abin da ya sa jam’iyyar ke fama da rashin tabbas a matakin ƙasa baki ɗaya.

Ita kuwa Jam’iyyar NDC, wadda ta tsayar da Peter Obi a takarar Shugaban Ƙasa tare da Rabi’u Kwankwaso a matsayin mataimaki, na ƙoƙarin kafa kanta a matsayin sabuwar jam’iyyar adawa da za ta ƙalubalanci APC, amma tana fuskantar ƙalubalen goyon baya da kuma matsalar haɗin kai a tsakanin shugabanninta.

Masu fashin bakin harkokin siyasa na ganin rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun adawa na iya ba wa jam’iyyar APC cikakkiyar dama a zaɓe mai zuwa, musamman idan har ’yan adawa suka gaza haɗa kai gabanin zaɓen.

Tuni jama’a suka sanya ayar tambaya kan batun binciken Atiku Abubakar da sabon binciken Abubakar Malami da aka gabatar wa Hukumar EFCC, kamar yadda rahotanni a watan Satumba suka bayyana cewa hukumar ta kafa tawaga ta musamman domin binciken wasu mu’amalolin kuɗi da suka shafi Atiku da tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami, dangane da hukuncin da Kotun Sasantawa ta Ƙasa da Ƙasa ta ICC da ke Paris ta yanke kan rikicin aikin samar da wutar lantarki a Mambilla.

Atiku da Malami sun bayyana cewa ba su da wani abin ɓoyewa game da sha’anin wutar Mambilla, kuma tayar da maganar a irin wannan lokaci na gabatowar zaɓe yana nuna yadda jam’iyya mai mulki ta kasa zaune ta kasa tsaye a ƙoƙarinta na yi musu bita-da-ƙulli da ɓata musu suna.

Sai dai hukumomin bincike sun musanta zargin, inda suka bayyana cewa suna gudanar da aiki ne bisa doka ba tare da la’akari da jam’iyya ba a yaƙin da suke yi da cin hanci da rashawa; a yayin da ita ma APC ta ce ko kaɗan ba ta da hannu a binciken da hukumomin ke gudanarwa.

Sakamakon ƙarfi da tasirin jam’iyyun adawa a matsayin babbar barazana ga jam’iyya mai mulki, tuni abokan hamayya suka zargi masu riƙe da madafun iko da amfani da hukumomin gwamnati wajen farautarsu domin hana su motsi.

Fagen siyasa ya ɗauki sabon salo, musamman yadda wasu manyan ƴan adawa da ke ƙalubalantar APC ke fuskantar binciken hukumomin gwamnati masu yaƙi da cin hanci gami da shari’o’i kan tuhume-tuhume daban-daban.

Wannan yanayi na siyasa ya haifar da tambayoyi daga abokan hamayya: shin ko matakan da hukumomin gwamnati ke ɗauka na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da doka, ko kuwa suna da alaƙa da ƙara matsin lamba ga abokan hamayyar siyasa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027?

Haka ma jagororin adawa sun bayyana cewa yunƙurin binciken tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar kan kwangilar wutar Mambilla ya samo asali ne daga yadda shugaban APC na Kudu-maso-Kudu, Hilliard Eta, ya buƙaci EFCC da sauran hukumomin tsaro su binciki Atiku kan zargin cin hanci da rashawa.

A watan Satumba, Atiku ya yi watsi da kiraye-kirayen binciken, yana mai cewa bita-da-ƙullin siyasa ne kawai a daidai lokacin da ake daf da zaɓe, sakamakon tsoron karɓuwarsa da jam’iyya mai mulki ke yi, wanda a kan haka take son raunata shi.

An tsare tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a ranar 16 ga Fabrairu, 2026, bayan ya amsa gayyatar EFCC domin yi masa tambayoyi kan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗen jihar lokacin da yake gwamna.

Hukumar EFCC ta bincike shi ne kan zargin karkatar da kusan Naira biliyan 423, kafin daga bisani ICPC ta sake tsare shi a ranar 18 ga Fabrairu domin ci gaba da bincike kan zargin halasta kuɗaɗen haram. Tsohon gwamnan yana ci gaba da zama a tsare na tsawon watanni bakwai.

Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya fara fuskantar tuhuma ne a ranar 8 ga Disamba, 2025, a lokacin da Hukumar EFCC ta gayyace shi inda take bincikensa kan zargin halasta kuɗaɗen haram da suka kai Naira biliyan 8.7, zargin da ya shafi shi, matarsa, da ɗansa.

Bayan an tsare shi a kurkukun Kuje, an sake kama shi a ranar 19 ga Janairu, 2026, jim kaɗan bayan ya cika sharuɗɗan beli. Haka kuma gwamnati ta samu nasarar ƙwace ƙadarorin Malami na biliyoyin naira a shari’ar da ake ci gaba da fafatawa a kai.

A yayin da ƴan adawa ke zargin gwamnati da yin amfani da hukumomin tsaro da bincike wajen matsa musu lamba, gwamnatin APC ta sha jaddada cewa hukumomin yaƙi da cin hanci da sauran jami’an tsaro suna gudanar da ayyukansu ne bisa tsarin doka, ba tare da la’akari da jam’iyya ko matsayin wanda ake bincika ba.

Haka kuma a watannin baya, wasu jam’iyyun adawa sun nuna rashin amincewa da naɗin Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe, inda suka bayyana cewa shugaban hukumar ya riga ya nuna ɓangaren da yake goyon baya, don haka ba su amince da sahihancin zaɓen da zai gudanar ba.

Gwamnatin
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Kotu Ta Yankewa Jami’an Tsaron Sa- Kai 3 Hukuncin Kisa A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Majalisar Sarkin Musulmi Za Ta Kafa Bankin Musulunci Don Yaƙi Da Talauci
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Ɗan Majalisa Zai Ɗauki Nauyin Biyan Ma’aikatan Da Gwamnatin Sakkwato Ta Riƙewa Albashi 
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Tambuwal Ya Yi Ƙarar Gwamnatin Sakkwato Kan Riƙe Rahoton Hukumar Bincike

MASU ALAKA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
Siyasa

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026
Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo
Siyasa

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

October 22, 2026
Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027
Siyasa

Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027

October 22, 2026
Next Post
Tattalin Arziƙin Nijeriya Zai Haɓaka Da Kashi 4.3% A Shekarar 2026 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Zai Haɓaka Da Kashi 4.3% A Shekarar 2026 - Bankin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.