ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwamitin Kamfen Ɗin APC Zai Gudanar Da Taronsa Na Farko A Kaduna

by Abubakar Sulaiman
5 days ago

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC (APC-PCC) ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na kamfen ɗin, Sanata Abdulaziz Yari, zai gudanar da taronsa na farko na share fage a birnin Abuja a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2026.

Wannan taro na da nufin tsara dabarun aiki da kuma kammala dukkan shirye-shiryen taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na babban zaɓen 2027 da za a yi a birnin Kaduna a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba.

A yayin taron na ranar Talata, ana sa ran kwamitin zai raba wa shugabannin sassan kamfen ɗin ayyukan da za su gudanar tare da tsara jadawalin yadda za a zagaya shiyyoyi daban-daban na ƙasar.

ADVERTISEMENT

Babban abin da za a fi mayar da hankali a kai shi ne tsara yadda manyan jiga-jigan jam’iyyar za su wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a tarukan gangami a jihohi sama da 20 da ba zai samu damar halarta da kansa ba, domin ba shi damar ci gaba da kula da harkokin gudanar da mulkin ƙasa a Abuja.

Kwamitin zai kuma tattauna hanyoyin tallata nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a shekaru uku da rabi da suka gabata, musamman sauye-sauyen tattalin arziƙin da suka fara haifar da sauƙin hauhawar farashin kaya zuwa kashi 14.63 cikin ɗari a watan Satumba, da kuma ayyukan more rayuwa.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

Haka kuma, taron zai fayyace dabarun mayar da martani ga kalaman jam’iyyun adawa irin su ADC da NDC, tare da sake jaddada aniyar jam’iyya mai mulki na gudanar da tsaftataccen kamfen na wayewar kai ba tare da amfani da kalamai masu zafi ko tayar da zaune-tsaye ba.

Wannan ganawa ta ranar Talata za ta zama tubalin fara ayyukan kamfen ɗin jam’iyyar gadan-gadan a faɗin ƙasar, inda ake sa ran gwamnonin jam’iyyar, ministoci, da ƴan majalisun tarayya za su halarta domin haɗa ƙarfi da ƙarfe.

Shugabannin APC sun nuna ƙwarin gwuiwar cewa taron na Kaduna zai nuna irin ɗimbin goyon bayan da jam’iyyar ke da shi a Arewa da Kudancin ƙasar, a daidai lokacin da take neman sabon wa’adin shekaru huɗu domin ciyar da Nijeriya gaba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC
  • Abubakar Sulaiman
    Taron Kaduna Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Arewa Maso Yamma Ga Tinubu — Musa Iliyasu

MASU ALAKA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna
Manyan Labarai

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume
Manyan Labarai

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Next Post
Babu Wani Harin Da Aka Kai Wa Mataimakin Gwamnan Zamfara — Kakakin Gwamna

Babu Wani Harin Da Aka Kai Wa Mataimakin Gwamnan Zamfara — Kakakin Gwamna

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.